Paulo Fonseca: An dakatar da kocin Lyon ta Faransa tsawon watanni 9

An hukunta kocin Lyon ta Faransa, Paulo Fonseca da haramcin watanni tara, bayan samun sa da laifin jayayya da alƙalin wasa a farkon Maris ɗin nan.

/ AFP

An samu kocin Lyon ta Faransa, Paulo Fonseca da laifin jayayya da alƙalin wasa, bayan wata ƙazamar gardama da suka yi bayan wani wasa da Lyon ta doke Brest da ci 2-1 a babbar gasar Faransa, Ligue 1.

Kocin ya tunkari alƙalin cikin fushi, inda ya kai kansa dab da fuskar alƙalin mai suna Benoit Millot. Daga bisani kocin ya ba da haƙuri, kafin hukunci ya biyo baya.

Fonseca, wanda tsohon kocin AC Milan ne, ya samu jan kati kai-tsaye yayin wasan da aka yi farkon Maris ɗin nan. Sannan a yanzu aka haramta masa wasa har na wata tara.

Hukuncin zai ƙunshi haramcin halartar filin wasa, da shiga ɗakin ‘yan wasa, da duk wani taro kan ƙwallo kafin, da yayin ko bayan duk wani wasa, har zuwa 30 ga Nuwamba.

Alƙalin da abin ya faru da shi, Millot ya yi magana game da halayyar Fonseca bayan wasan: "Ya yo kaina yana mai barazana, kuma na yanke hukuncin sallamar sa daga fili. Hancin junanmu ya ɗan taɓu. [Abin] barazana ce, kuma mummunar halayya ce da ba a sa ran ganin ta daga ƙwararren koci."

Mummunar halayya

  • Shugaban kwamitin ladabtarwar, Sebastien Deneux ya ce: "Hukumar ƙwallo ta yi tir kan cewa, an sake samu wani jami’i a gasar Ligue 1 da ya zaɓi wannan halayya, sannan ya yi watsi da buƙatar kyakkyawar ɗabi’a.”
  • Ya ƙara da cewa, “Kwamitin ya yanke cewa halayyar Mr Fonseca ta kai kansa gaban alƙalin wasa, da yi masa tsawa, har ta kai sun kusa yin karo da kai, halayya ce ta barazana."
  • Fonseca ya zo Lyon a Janairu bayan da AC Milan ta sallame shi. Sai dai bai fara aiki da sa’a ba, sai dai za a jira a gani ko dakatarwar za ta shafi ƙungiyar tasa. Lyon tana mataki na shida a teburin Ligue 1, kuma za ta kara da FCSB nan gaba a gasar Europa League.