Gwamnonin Kudu maso Yammacin Nijeriya sun sabunta kira kan samar da ‘yan sandan jihohi

Gwamnonin sun kuma amince da kafa wata kafa ta intanet ta musayar bayanan sirri kan barazana da kuma tsaro sakanin jihohin.

By
Gwamnonin Jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya

Gwamnonin Kudu maso yammacin Nijeriya sun sabunta kira na samar da ‘yan sandan jihohi domin daƙile matsalolin tsaro da yankin da ma ƙasar baki ɗaya ke fama da su.

Sun yi wannan kiran ne ranar Litinin a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, bayan sun yi wani zama na sirri a ofishin gwamnan jihar Oyo.

Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da shugaban ƙungiyar kuma gwamnanm jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Saunran sun haɗa da Dapo Abiodun (gwaman jihar Ogun) da Lucky Aiyedatiwa (gwamnan jihar Ondo) da Biodun Oyebanji (gwamnan jihar Ekiti) da kuma mai masauƙin baƙi, Seyi Makinde (gwamnan jihar Oyo).

Sai dai kuma gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya samu wakilcin mataimakinsa, Kola Adewusi.

Gwamnonin sun yi ba’asi kan damuwar da ake samu kuma suka tsara martani na haɗaka cikin rashin tsaro da ƙarin fargabar da ake samu a kudu maso yammacin Nijeriya.

Sanwo-Olu ne ya karanta saƙon bayan taron bayan taron na sirri da suka shafe sa’o’i suna yi.

Asusun tsaro

Gwamnonin sun mayar da hankali kan haɗin kan yankin kuma sun amince da kafa wani asusun tsaro domin ƙarfafa martanin yankin ga rashin tsaro, musamman kan ƙarin garkuwa da mutane da haƙar ma’dinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma tafiye-tafiye tsakanin jihohi babu ƙaƙƙautawa.

Kazalika ƙungiyar ta ce asusun zai kasance a ƙarƙashin jagorancin hukumar da ke kula da ƙadarorin tsohuwar jihar yammacin Nijeriya (DAWN) ne da kuma sa ido na masu ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro a jihohin shida.

Ta ce asusun zai taimaka wajen ayyukan tsaron na haɗin gwiwa da musayar bayanan sirri da kuma ɗaukar matakai cikin sauri a cikin jihohin Legas da Ogun da Oyo da Ondo da Osun da kuma Ekiti.

Gwamnonin sun kuma bayyana damuwarsu kan ci rani babu ƙaƙƙutawa tsakanin jihohi, suna masu kira da a sake matsa kaimi wajen sa ido kan bakin iyakoki da kuma aiki da hukumar tattara bayanain ‘yan Nijeriya (NIMC) domin tabbatar da cewa an gane ‘yan ci rani da kuma hana shigar masu laifi.

Da take nuna tashin hankali game da ƙaruwar haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, gwamnonin sun yi kira da a ƙarfafa tsarin tantancewa wajen ba da lasisin da kuma matsa kaimi wajen ƙaddamar da dokar hana haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba domin daƙile barazanar yanayi da tsaro waɗanda aka alaƙanta da haƙr ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba

Game da tsaron cikin dazuka kuwa, gwamnonin sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka wajen tura masu gadin gazuka a fadin ynakin domin ƙwace dazukan da masu aikata laifuka ke a,mfani da su a matsayin mafaka.

Ganawar da gwamnonin na zuwa ne bayan hare-hare na baya bayan nan da ‘yan bindiga suka kai wasu jihohin arewacin ƙasar.

A jihar Kebbi ‘yan bindiga sun sace ‘yan mata ɗalibai 25 daga makarantar gwamnati ta mata a garin Maga inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar.

A jihar Neja kuwa sun sace sama da yara 300 a makaranatar  St. Mary ta ɗarikar Katolika da ke Papiri.

A makon da ya gabata an kashe mutum uku a lokacin da ‘yan bindiga suka saci masu ibada a lokacin wani hari a coci da ke garin Eruku na jihar Kwara.

Ranar Lahadi, ‘yan sanda sun tabbatar da kashe ‘yan sanda biyar a jihar Bauchi da kuma garkuwa da mata 12 a jihar Borno.