| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
TikTok da Youtube sun rufe shafukan yara miliyan 4.7 a Indonesia bayan matakan gwamnati
‘Mun jaddada cewa babu kofar ja da baya game da aiki da matakin,"‘ in ji Ministan Sadarwa Hafid.
TikTok da Youtube sun rufe shafukan yara miliyan 4.7 a Indonesia bayan matakan gwamnati
Matakin ya fara aiki a ranar 28 ga Maris kuma ana aiwatar da shi a mataki-mataki a fadin kasar. / AP

Ministan sadarwa na Indonesia ya ce kamfanonin sada zumunta na TikTok da YouTube sun rufe jimillar shafukan yara 'yan ƙasa da shekara 16 a Indonesia miliyan 4.7, yayin da takunkumin da aka sanya wa shafukan sada zumunta ya fara aiki.

TikTok, wanda kamfanin fasaha China ByteDance ya ƙirƙiro, ya rufe shafuka miliyan 4.1, yayin da YouTube mallakin Google ya rufe shafuka 600,000, in ji Ministan Sadarwa da Fasaha Meutya Hafid a daren Alhamis, yana mai ƙara wa da cewa ma'aikatar tana son sauran shafukan sada zumunta su bi sahun wadannan.

Babu ɗaya daga kamfanonin da ya bayar da amsa nan take ga buƙatar yin tsokaci kan batun.

A watan Maris, Indonesia ta fitar da wata doka wadda ta buƙaci kamfanonin sada zumunta waɗanda ke da dandamali da take ganin suna da babban hatsari kan su rufe shafukan yara 'yan ƙasa da shekara 16, waɗanda zuwa yanzu sun haɗa da X, Instagram na Meta da kuma Roblox na wasannin yanar gizo.

"Ba wai kawai muna jinkirta samun damar yara ba ne, har ma muna son halaye daga shafukan su ma su canza," in ji Meutya a ranar Alhamis, yana mai ƙara wa da cewa ma'aikatar tana duba rahotannin tantance kai na kamfanonin.

Tsarin da Indonesia ta ɗauka, wanda gwamnati ta ce an yi shi ne don rage hatsarin cin zarafi ta yanar gizo da maitar amfani da da ita, ya biyo bayan haramcin da aka yi a Australia a bara saboda damuwa game da illolin da kafofin sada zumunta ke iya haifarwa ga lafiyar kwakwalwar matasa.

Ana sa ido sosai kan matakin farko na Australia mai ban mamaki, inda ƙasashe a duniya ke neman yin koyi da shi a cikin damuwa game da lafiyar kwakwalwa da ta jiki na yara ƙanana.

Birtaniya ta sanar a wannan watan cewa ta tsara wasu hani da suka haɗa da wasanni da shafukan watsa bidiyo kai tsaye.