Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da shugabancin David Mark na Jam’iyyar ADC inda ta soke umarnin da Kotun Daukaka Ƙara da ke Abuja ta bayar a cikin rikicin shugabancin jam’iyyar adawar.
Wannan hukunci ya dawo da kwamitin zartarwa da David Mark ke jagoranta, wanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta taɓa cirewa daga rajista.
A cikin hukunci guda ɗaya da dukkan alkalan kwamitin biyar suka amince da shi a ranar Alhamis, wanda Mai Shari’a Mohammed Lawal Garba ya jagoranta, Kotun Kolin ta bayyana cewa umarnin da Kotun Daukaka Ƙara ta bayar ba shi da amfani kuma ba a buƙatarsa.
Kotun Koli ta kuma bayyana cewa an shigar da ƙarar da ta shafi batun “ikon shari’a” ne bisa umarnin kotu na wucin gadi da ke kiran ɓangarorin su bayyana dalili, ba tare da an fara samun izinin Kotun Daukaka Ƙara ba.
An daɗe ana kai ruwa rana a kan batun shugabancin Jam’iyyar ADC inda ɓangaren David Mark wanda shi jiga-jigan jam’iyyar irinsu Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso da Aminu Waziri Tambuwal ke mara wa baya, da kuma ɓangaren Nafiu Bala da ya dage cewa shi ne shugaban jam’iyyar.
Lamari ya kaɗa hantar manyan ‘yan ADC waɗanda suke ganin idan har ba su yi nasara a Kotun Ƙoli ba to hakan ka iya zama cikas gare su musamman bayan yin gamayyarsu wacce suke ganin za ta iya kai su ga kawar da Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya, kamar yadda masana suka ce.















