Jami’an tsaron Nijeriya sun kama wani mutum mai suna Ifechukwu Dennis da ake zargi da ƙirƙira da yada wani sautin murya na bogi da aka yi ta amfani da ƙirƙirarriya basirar, AI, wanda aka gabatar a matsayin muryar Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga ya ce tawagar musamman ta Sufeto Janar na ‘yansanda ce ta kama Dennis a birnin Benin da ke Jihar Edo. Ya kara da cewa ‘yansanda za su fitar da cikakken bayani kan lamarin.
Rahotanni sun ce sautin muryar bogin ya yi kama da muryar Shugaba Tinubu, inda aka sanya shi yana yin kalamai kan matsalolin tsaro, jam’iyyun adawa da kuma zaben shekarar 2027.
Bidiyon da ke dauke da wannan sauti ya bazu sosai a shafukan sada zumunta, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi a fadin kasar.
Fadar Shugaban Kasa ta musanta sahihancin sautin tun bayan fitowarsa, tana mai cewa an kirkire shi ne domin yaudarar ‘yan Nijeriya.
Haka kuma ta gargadi jama’a da su rika tantance sahihancin bayanai kafin yada su, musamman yayin da kasar ke tunkarar zaben 2027.
Lamarin ya sake jawo hankali kan yadda ake amfani da fasahar AI wajen samar da bayanan karya da kuma kalubalen da hakan ke haifarwa ga siyasa da tsaron bayanai a Nijeriya.











![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)
