Amsar tana tattare da rawar da zinare ke takawa a matsayin ma'ajiyar kadara, shinge daga hatsari da kuma alamar aminci lokacin da imani da tsarin siyasa da sha’anin kuɗi ya raunana. Sau da yawa ana kwatanta zinare a matsayin kadara mai aminci.
Ba kamar tsabar kuɗi ba, babu wata gwamnati da ke samar da shi. Ba kamar takardun lamuni ba, bai dogara da sahihancin mai karɓar bashi ba kuma ba kamar hannun jari ba, ƙimarsa ba ta da alaƙa da ribar kamfanoni ko ci gaban tattalin arziki.
Rikicin siyasa yana haifar da rashin tabbas game da iyakoki, hanyoyin kasuwanci, samar da makamashi har ma da makomar gwamnatoci da kansu.
Masu zuba jari, 'yan kasuwa da manyan bankunan kasashe suna mayar da martani ta hanyar rage ta’ammali da kadarorin da ke da hatsari kamar hannun jari ko kuɗaɗen kasuwa masu tasowa.
A maimakon haka, jari yana tafiya zuwa ga kadarorin da ake ganin suna da karko kuma an yarda da su a ko'ina. Zinare ya fi dacewa da wannan bayanin fiye da kusan kowace irin haja.
Tun daga dawowar Trump mulki a 2024 zuwa ga daduwar rikcin kasuwanci da yaki a yankuna, kasuwannin duniya na kara sauyawa. A lokuta rashin tabbas irin haka, ana daukar zinare a matsayin kadarar kudi, wajen ajiya da za a jira har sai an samu sauki.
Tasirin mafaka mai tsaro
A lokutan kwanciyar hankali, wannan yana sa ya zama abin jan hankali, zama koma bayan hannun jari masu tasowa. Amma lokacin da siyasa ta tayar da rikici, tunanin takunkumi, juyin mulki, ko rikicin zaɓe, waɗannan abubuwa suna komawa kamar manyan ƙasashe masu ƙarfi.
Manyan jari na guje wa kasuwanci masu hatsari kamar kasuwancin lamuni da ke tasowa ko hannun jarin fasaha masu sauyawa, suna kwarara zuwa kadarorin da ke yin habaka cikin aminci. Zinare ya dace daidai da hakan, an yarda da shi a duk fadin duniya, ba za a iya ƙara tayar da farashinsa ba, kuma ana iya duakar sa cikin sauki zuwa kan iyakoki.
Kanun labarai na baya-bayan nan sun nuna hakan. 'Yan makonni da suka gabata, a tsaka da barazanar harajin Trump ga Greenland da matsin lamba ga Fed, zinare ya kafa tarihin kai wa fiye da $4,600 a kowane awo, mafi girman hauhawarsa a cikin shekaru da dama. Masu zuba jari ba sa yin cacar canke a kan "yawan amfanin" zinare; suna tserewa abin da ba a sani ba.
Abubuwan da suka faru kwanan nan sun nuna wannan a sarari. Lokacin da rikicin siyasa ya ta’azzara saboda sabbin haraji da matsin lamba akan manyan bankunan kasashe, farashin zinare ya tashi zuwa mataki mafi girma. Masu zuba jari ba sa neman kuɗi ko rabon riba; suna kare kansu daga hatsarin fada wa asara.
A lokacin da kudade suka karye
Babu wani abu da ke ƙara farashin zinare da sauri fiye da raunin kuɗi. Rikicin siyasa sau da yawa yana haifar da takunkumi, matsalolin bashi, da kashe kuɗi na gaggawa. Gwamnatoci suna mayar da martani ta hanyar buga kuɗi, wanda ke rage ƙarfin sayen kayayyaki.
Zinare yana tafiya akasin haka. Ana fitar da farashinsa a duniya da dalar Amurka, yana riƙe da darajarsa lokacin da kuɗaɗen gida suka faɗi. Wannan shi ne dalilin da ya sa zinare ke zama abin sha'awa musamman a ƙasashen da ke fuskantar hauhawar farashi ko rashin daidaiton kuɗi.
Manyan Bankunan kasashe sun fahimci wannan sosai. China ta ci gaba da ƙara yawan ajiyar zinarenta tun daga 2013, inda ta ƙara fiye da tan 1,000 zuwa 2023. Rasha da India sun bi irin wadannan hanyoyi.
A shekarar 2025, manyan bankunan kasashe sun sayi zinare a matakan da suka gabata, wanda ke nuna faɗaɗa himma ga 'yancin kai na kuɗi yayin da tashin hankali na siyasa ke ci gaba.
Targaden hauhawar farashi da jigilar kayayyaki
Rashin zaman lafiya na siyasa sau da yawa yana kawo hauhawar farashi. Yaƙe-yaƙe suna kawo cikas ga ayyukan jigilar kayayyaki, suna ƙara farashin makamashi, kuma suna ƙara kashe kuɗi ga gwamnati. Don biyan kuɗi, kasashe na faɗaɗa samar da kuɗi, suna runanata adana kudade.
Zinare yana ba da kariya saboda wadatarsa tana ƙaruwa a hankali, kusan kashi 1-2% ne kawai a kowace shekara ta hanyar haƙar ma'adinai. Ba kamar kuɗaɗe ba, babu wani babban banki da zai iya ƙirƙirar ƙarin zinare cikin dare ɗaya.
Gwamnatoci suna buga kuɗi don cike gibi, suna karar da kudaden da suka adana. Zinare yana magance wannan, wadatarsa tana ƙaruwa da kashi 1-2% kowace shekara ta hanyar haƙar ma'adinai, inda yake da kariya daga injinan buga kudi na manyan bankuna.
A tarihi, lokacin da hauhawar farashi ya wuce yawan kuɗin da ake samu, zinare yana ƙaruwa. A Amurka a China ma farashin karuwa, ana mats alambar haraji yayin da a Gabas ta Tsakiya ma ake shaida hakan.
Masana tattalin arziki yanzu suna kallon zinare yana iya kai wa dala $3,150 kowane awo nan da 2051 a ƙarƙashin manufofin Trump, wanda rage ƙa'idoji da rikicin ciniki ke haifarwa wanda zai iya haifar da hauhawar farashi a duniya.
Wannan ba hayaniya ba ce, dabarar gano tsari ce. Tsawaitawar rashin kwanciyar hankali ba wai kawai yana ƙara farashi a cikin ɗan gajeren lokaci ba ne, har ma yana ƙara habaka zinare a matsayin babban jari.
Ilimin halayyar dan adam da tsoro
Bayan tattalin arziki, zinare yana amfana daga ilimin halayyar ɗan adam. Tsawon dubban shekaru, zinare yana wakiltar tsaro daga dauloli na da zuwa waɗanda suka tsira daga rikicin zamani. Lokacin da tsoro ya yaɗu, mutane suna koma wa ga abin da ya yi aiki a baya.
Jefa kuri'ar Brexit a 2016 misali ne bayyananne. Fam na Birtaniya ya faɗi da ƙarfi cikin dare ɗaya, yayin da farashin zinare ya yi tashin gwauron zabi ba saboda sabbin bayanai ba, amma saboda tsoro da rashin tabbas.
Darussa daga rikice-rikicen baya bayan nan
Daskarar da asusun ajiyar kuɗi na ƙasashen waje na Rasha a shekarar 2022 ya aika da saƙo mai ƙarfi ga duniya. Ana iya kwace kadarorin kuɗi da aka ajiye a ƙasashen waje. Zinare, wanda aka adana a cikin gida, ba zai iya ba.
Sakamakon haka, ƙasashe da yawa sun hanzarta tara zinarensu. Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China, takunkumi, da hamayyar siyasa duk sun ƙarfafa rawar zinare a matsayin wata ma'ajiyar daraja ta tsaka-tsaki.
Duba ga dogon lokaci
Waɗannan sauye-sauyen siyasa ba na ɗan lokaci ba ne. Amincewa da cibiyoyin duniya ya ragu, kuma ana tantamar dogaro da kadarorin gargajiya masu aminci. Manyan Bankuna na sayen zinare fiye da yadda ma'adanai za su iya samarwa, wani yanayi da ake sa ran zai ci gaba har zuwa shekaru goma masu zuwa.
Hasashe ya nuna cewa farashin zinare na iya ƙaruwa yayin da rashin zaman lafiya ya zama sabon abu. Zinare na iya zama tsohon yayi, amma tarihi ya tabbatar da darajarsa. Lokacin da siyasa ta lalata kasuwanni kuma kuɗi ya rasa aminci, zinare ya kasance kamar yadda yake a koyaushe. Kadara mai ɗorewa akan aminci.
Marubuciyar, Hafsa Abdiwahab Sheikh, 'yar jarida ce mai zaman kanta kuma mai bincike da ke mai da hankali kan siyasar Gabashin Afirka.
Togaciya: Ba lallai ne ra’ayoyin da marubucin ya bayyana su yi daidai da ra’ayoyin dab’i na TRT Afrika ba.












