| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya za ta fara sarrafa kayayyakin tsara iyali a cikin ƙasar
Yayin da yake ƙaddamar da kwamitin a Abuja, Pate ya ce jama’ar ƙasar su ne kadarar ƙasar mafi girma kuma dole a sauya su zuwa albarkatu masu samar da abubuwa da za su iya kawo ci-gaba da wadatar ƙasar.
Gwamnatin Nijeriya za ta fara sarrafa kayayyakin tsara iyali a cikin ƙasar
Farfesa Muhammad Ali Pate, Ministan lafiyar Nijeriya / Facebook/Muhammad Ali Pate

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce za ta fara sarrafa abubuwan tsara iyali a cikin ƙasar domin ƙarfafa lafiyar jama’ar ƙasar da kuma amfani da jama’ar ƙasar mai yawan matasa a matsayin abin haɓaka tattalin arziki mai dorewa.

Wata sanarwar mataimakin daraktan watsa labarai da hulɗa da jama’a na ministan lafiyar Nijeriya, Prof. Muhammad Ali Pate, Ado Bako, ya fitar ranar Jumma’a ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar ta kafa wani kwamiti tsakanin ma’aikatun gwamnati domin ciyar da shirin gaba, kamar yadda kafar Channels ta Nijeriya ta ruwaito.

Farfesa Pate ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki ga Nijeriya da ma sauran yankin Afirka kudu da Sahara, yana mai jaddada cewa sarrafa kayayyakin a cikin gida zai rage dogaro kan kayayyakin da ake shigowa da su da samar da ayyukanyi ga matasa ‘yan Nijeriya da kuma samar da kima ta tattlin arziki a cikin ƙasar.

Yayin da yake ƙaddamar da kwamitin a Abuja, Pate ya ce jama’ar ƙasar su ne kadarar ƙasar mafi girma kuma dole a sauya su zuwa albarkatu masu samar da abubuwa da za su iya kawo ci-gaba da wadatar ƙasar.

Ministan lafiyar ya ce an kafa dandalin kwamitin ne da zummar cim ma fatan Shugaba Tinubu na samar da Nijeriya mai wadata da zaman lafiya da ya mayar da hankali kan mutane, yana mai jaddada cewa yawan jama’ar Nijeriya da ke daɗa ƙaruwa zai iya zama muhimmiyar kadara ko kuma nauyi dangane da irin jarin da aka zuba a kiwon lafiya da ilimi da ƙarfafa mutane da kuma yanayin ayyuka.

Ya ce Nijeriya, wadda take da kimanin yawan mutane da suka kai miliyan 230 million kuma yawnacinsu matasa ne, inda take ƙara miliyoyin mutane zuwa cikin yawan jama’arta a ko wace shekara kuma an yi kiyasin cewa adadin mutane ƙasar zai kai miliyan 450 zuwa miliyan 500 nan da shekarar 2050.

Saboda haka ministan ya jaddada bukatar da ke akwai ta zuba jari da gangan wajen inganta jarin rayuwar mutane don tabbatar da cewa adadin jama’r da ke ƙaruwa yana da lafiya da ilimi da ƙwarewa da kuma iya samar da ababe ga tattalin arziki.

Pate ya bayyana cewa kwamitin na tsakanin ma’aikatu zai yi amfani da hanya ta iya rayuwa inda ya tara hukumomin gwmanati masu alaƙa su magance matsalolin ‘yan Nijeriya tun daga matakin balaga zuwa lokacin da suka gama girma suka zama iyaye kuma suka tsufa, yana mai cewa ko wace hukuma da ke cikin tsarin akwai aikin da zai yi wajen cim ma burin kwamitin.

Rumbun Labarai
Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan 'yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu
FBI ta nemi haɗin kan EFCC don gudanar da bincike kan zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin Amurka
Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu
Tinubu ya bai wa kowace 'yar tawagar ƙwallon kwandon Nijeriya dala dubu ɗari-ɗari
Mutum 511 sun kamu da cutar mashaƙo a Jihar Yobe a Nijeriya
Amurka ta aika sabbin kayayyakin soji Nijeriya
Zaben Nijeriya na 2027: Matakan Tinubu na rage talauci da alƙawarin Atiku na mayar da tallafin fetur
Jakadan Nijeriya ya ziyarci ’yan kasar 198 da ke gidan yari a Indiya
Mutane da dama sun mutu yayin da wasu ke asibiti bayan sun sha wani maganin gargajiya a jihar Ondo
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta kama wasu mutane da kudade da ake zargin kuɗin fansa ne
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano
Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan yaƙi da ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram
NEMA ta karɓi ’yan Nijeriya 180 da aka mayar da su gida daga Libya
Sojojin Nijeriya sun kama wasu da ake zargin masu kai wa ’yanta’adda kayayyaki ne a Jihar Yobe
FIFA ta tura tawaga zuwa Nijeriya don gano ko gwamnati ta tsoma baki a murabus ɗin shugabannin NFF
INEC za ta ƙaddamar da na’urar bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai-tsaye
An  kashe mutum 12, an jikkata 2 a sabon harin da Boko Haram ta kai wani ƙauye a Adamawa ta Nijeriya
‘Yanbindiga sun kashe mutum 10, sun sace 40 a wani ƙauyen Sokoto
Gwamnatin Jihar Filato a Nijeriya ta rufe makarantu saboda ɓarkewar cutar mashaƙo
NDC ta yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa kan ba ta da ’yan takarar gwamna a jihohin Nijeriya 12