Gidauniyar Turkiyya ta ba da tallafin abinci ga iyalai 8,250 da iftila’in fari ya shafa a Somaliya

Somaliya na fuskantar ƙarin matsalar tsaron abinci da rashin abinci mai gina jiki, inda kimanin mutane miliyan 6.5 ke fuskantar tsananin yunwa.

By
Tun daga shekarar 2017, EU ta samar da tallafin jinƙai na fiye da dala miliyan 817 ga Somaliya, in ji sanarwar. / TRT Afrika Hausa

Wata kungiyar agaji ta Turkiyya ta kai tallafin abinci ga iyalai 8,250 a yankunan da fari ya shafa a Somaliya a lokacin watan Ramadan mai tsarki, in ji jami'an Turkiyya.

Gidauniyar Turkiyya Diyanet (TDV) ta rarraba kayan abinci a jihohi bakwai da yankuna 13 na ƙasar Somaliya a matsayin wani bangaren shirinta na ba da agaji a watan Ramadan, wanda ke samun gudummawa daga masu ba da sadaƙa.

An shirya kayan tallafin ne ga iyalai da ke fama da matsalar tattalin arziki a yanayi iftila’in fari mai da aka kwashe tsawon lokaci ana fuskanta kana ya kara muni a 'yan shekarun nan.

Tawagogi da suka kunshi ma'aikatan gidauniya da masu sa kai ne suka yi rabon kayan abinci a yankuna daban-daban, ciki har da sansanonin da ke babban birnin Mogadishu.

An gudanar da tarukan ba da tallafin a sansanin Hindere da ke gundumar Daynile da kuma sansanin Bilhayr da ke yankin Garapaley, inda jami'ai suka gana da iyalai da lamarin ya shafa bayan sun ƙarbi kayayyakin.

Omer Faruk Arslan, mai ba da shawara kan ayyukan addini a Ofishin Jakadancin Turkiyya da ke Mogadishu, ya ce tallafin jinƙan yana da matukar muhimmanci yayin da iftila’in fari ya yi tsanani a fadin Somaliya.

"A cikin shekaru 2, an samu matsaloli masu tsanani a fannin samun abinci da ruwa sakamakon fari," in ji Arslan "amma ta hanyar tallafin masu ba da sadaka, muna kaiwa masu buƙata kayan abinci yankuna 13."

Tallafin EU ga Somaliya

A ranar Alhamis, ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta sanar da ba dala miliyan 74 a matsayin tallafin jinƙai don tallafawa al'ummomin da ke cikin mawuyacin hali a faɗin Somaliya yayin da ƙasar ke fama da iftila’in "fari mai tsanani, da kuma rikice-rikicen da ake ci gaba da fuskanta, gami da ƙaura da kuma hauhawar farashin abinci."

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar EU ta ce tallafin zai fi mayar da hankali wajen ayyukan ceton rai, gami da na kiwon lafiya da abinci masu gina jiki, da tallafin kuɗi na gaggawa, da ayyukan ruwa da tsaftar muhalli, da shirye-shiryen kariya, da kuma ilimin gaggawa.

Somaliya na fuskantar ƙarin matsalar tsaron abinci da rashin abinci mai gina jiki, inda kimanin mutane miliyan 6.5 ke fuskantar tsananin yunwa, a cewar sanarwar.

Binciken jinƙai ya nuna cewa kimanin yara miliyan 1.85 'yan ƙasa da shekara biyar suna cikin haɗarin kamuwa da tsananin matsalar rashin abinci mai gina jiki.

EU ta ce za a bayar da taimakon ta hanyar abokan hulɗa na jinƙai da aka amince da su waɗanda ke aiki a ƙasa don tabbatar da cewa taimakon ya isa ga waɗanda abin ya cancanta akan lokaci, tare da haɗin kai da kuma aminci.

Tun daga shekarar 2017, EU ta samar da tallafin jinƙai na fiye da dala miliyan 817 ga al’ummar Somaliya, in ji sanarwar.