| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 18 a arewa maso-gabas, in ji rundunar soji
Dakarun Njeria sun kashe a kalla ‘yan ta’adda 18 tare da lalata mafakar ‘yan ta’adda da dama a wasu farmakai da aka tsara kai wa a fadin jihar Borno, in ji rundunar sojin kasar a ranar Laraba.
Dakarun Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 18 a arewa maso-gabas, in ji rundunar soji
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda a kalla 18 a wani babban farnaki a yankin arewa maso-gabashin kasar. / Reuters / Reuters

Sojojin Najeriya sun kashe a kalla 'yanta'adda 18 tare da lalata wasu sansanonin 'yanta'adda da dama a farmakan da aka tsara kai wa a fadin jihar Borno, in ji rundunar a ranar Laraba, yayin da jami'an tsaro ke kara matsin lamba kan kungiyoyin 'yan ta'adda a arewa maso-gabas.

Jihar Borno na barazana daga 'yan ta'addar Boko Haram tsawon shekaru 17. Hare-haren ta'addanci a jihar sun kashe dubban mutane tare da raba kimanin miliyan biyu da matsugunansu.

Kakakin rundunar sojin sama Sani Uba ya ce sojoji da ke aiki tare da rundunonin sojojin sama da masu taimakawa na yankin sun kai hare-hare a yankin Timbuktu da dajin Bulabulin, inda suka kai hari kan mafaka da hanyoyin samar da kayayyakin ‘yn ta’addar.

An kashe 'yan ta'adda 11 a Bulabulin da bakwai a yankin Timbuktu, in ji Uba a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Farmakin na da manufar kawar da barazanar ‘yan ta’adda

Farmakan sun kasance wani ɓangare na wani gangami da ake yi da nufin wargaza wuraren da 'yan ta'adda ke da iko da su a yankin bayan wani hari da aka kai kwanan nan kan sansanonin sojoji wanda ya kashe sojoji da dama, ciki har da manyan hafsoshi.

Tallafi da jiragen sama ya bayar da damar sa ido da kuma kai hare-hare na musamman, yayin da ake ci gaba da kai farmakan bin diddigin 'yan ta'adda da suka tsere, in ji Uba.