Rasha ta yi iƙirarin cewa 'yan kwangilar sojin Faransa na da yawa a Afirka

Rasah ta ce 'yan kwangilar suna ɗaukar mayaƙan sa-kai domin shiga yaƙin Ukraine.

By
Maikatar ta ambato sunayen wasu sanannun kamfanonin soji masu zaman kansu na Faransa . / AA / AA

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta yi iƙirarin cewa kamfanonin soji masu zaman kansu na Faransa suna aiki a ƙasashen Afirka 14 inda kimanin 100 ke aiki a ƙetare.

Ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa cewa waɗannan kamfanonin yawanci tsofaffin hafsoshin jandarmomi ne ke jagorantar su, kuma a wasu lokuta jami’an leƙen asiri ne da suka yi ritaya.

“A halin yanzu, waɗannan kamfanonin kwangilar sojin suna aiki a Ukraine da Brazil da Brunei da India da SIifaniya da Qatar da Kuwait da Malaysia da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Singapore da Thailand da Philippines da Finland da Switzerland da Estonia da ƙasashen Afirka 14, ciki har da ƙasar Algeria da Benin da Gabon da Djibouti da Côte d’Ivoire da Mauritania da Nijeriya da Maroko da Senegal da Somalia da kuma Chadi,” in ji sanarwar.

Yawancin kamfanonin ana kafa su na wani ƙayyadadden lokaci domin yin wasu ayyuka, in ji sanarwar.

‘Horaswa domin yaƙi’

“A yanayin yaƙin Ukraine, kamfanonin kwangilar sojin Faransan suna yin ayyuka irin na horas da dakarun sojin Ukraine a ƙasashen gabashin Turai,” a cewarta.

Tun shekarar 2022, kamfanonin kwangilar sojin Faransa suka fara ɗaukar ‘yan sa-kai domin shiga yaƙi a Ukraine, inda suka ba da fifiko ga jami’ai daga dakarun ƙetare da tsofaffin jami’an tsaron Tarayyar Turai da ‘yan ƙasashen Afirka, a iƙirarin ma’aikatar.

Ma’aikatar ta ce ayyukan kamfanonin na samun jagorancin hukumar yaɗa bayanan fasaha ne.

Gwamnatin Faransa ce ke tabbatar da inda za a bai wa fifiko a waɗannan ayyukan kuma ita ce ke da mafi yawan iko a kansu ta hanyar masu shiga tsakani, in ji sanarwar.

Hukumomin Faransa ba su mayar da martani ga wannan iƙirarin na Rasha ba.