| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
An rufe coci-coci 50 da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a Kamaru
Tun a watan jiya ne shugaban MINAT, Paul Atanga Nji, ya sanar da shirin rufe coci-cocin bisa ƙorafi da ake yi kan hayaniya da zamba da ɗaiɗaita iyali.
00:00
An rufe coci-coci 50 da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a Kamaru
An rufe coci-cocin ne bayan an yi koke da hayaniya da zamba da kuma ɗaiɗaita iyali / Reuters
17 Maris 2025

Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru sun kulle coci-coci hamsin da aka gina ba bisa ƙa’ida ba a babban birnin ƙasar Yaounde.

Rahotanni daga ƙasar Kamaru sun ce ma’aikata daga ma’aikatar tsare-tsare da gudanar da garuruwa ta ƙasar (MINAT) ne suka rufe coci-cocin yayin da suka kai samame kan wuraren ibadan da aka gina ba bisa ƙa’ida ba.

Kamfanin dillacin labarai na Cameroon News Agency ta ambato DPO na Yaounde na biyu, Daouda Ousmanou, da ya jagoranci aikin yana cewa matsalolin da suka fuskanta sun haɗa da gudanar da coci-coci a cikin gidaje da kuma wurare masu hatsarin gaske.

Ya yi kira ga coci-coci su bi doka ko kuma su fuskanci hukuncin da zai biyo bayan rashin bin doka.

Kazalika mako biyu da suka wuce aka ruwaito cewa an rufe coci-coci 188 a ɓangare na IV na Yaounde a ƙarƙashin jagorancin DPO Elvis Akondi Mbahangwen saboda rashin takardun da ake buƙata.

Tun watan jiya ne dai shugaban MINAT, Paul Atanga Nji, ya sanar da shirin rufe coci-cocin bisa ga ƙorafi da ake yi kan hayaniya da zamba da ɗaiɗaita iyali.