| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Tinubu ya sauke Ministan Kuɗi Edun Wale Edun da na Gidaje Ahmad Dangiwa ya ba da sunan wasu sabbi
A cewar wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ya sanya wa hannu, Ministan Kuɗi kuma Mai kula da tattalin arziki, Wale Edun, da kuma Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmed Musa Dangiwa, sun bar mukamansu.
Tinubu ya sauke Ministan Kuɗi Edun Wale Edun da na Gidaje Ahmad Dangiwa ya ba da sunan wasu sabbi
Tinubu / Nigeria Presidency

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da wani ƙaramin sauyi a majalisar ministocinsa (FEC), wanda ya haifar da sauke wasu ministoci biyu da kuma nada sababbin waɗanda za su maye gurbinsu.

A cewar wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ya sanya wa hannu, Ministan Kuɗi kuma Mai kula da tattalin arziki, Wale Edun, da kuma Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmed Musa Dangiwa, sun bar mukamansu.

An umurci Edun da ya miƙa ragamar aiki ga Taiwo Oyedele, wanda aka ɗaga matsayinsa daga ƙaramin Minista zuwa babban Ministan Kuɗi kuma Mai kula da tattalin arziki.

Haka kuma, an bayyana Muttaqha Rabe Darma a matsayin wanda aka naɗa don zama Ministan Gidaje da Raya Birane, yayin da aka umarci Dangiwa da ya miƙa aiki ga karamin Minista ma’aikatar.

Sanarwar ta ce dole ne a kammala dukkanin miƙa mulki kafin ƙarshen aiki na ranar 23 ga Afrilu, 2026.

Akume ya bayyana cewa an yi wannan sauyi ne domin ƙarfafa haɗin kai da inganta aiki a gwamnati, tare da tabbatar da sakamako mai tasiri a fannin tattalin arziki bisa manufar “Renewed Hope Agenda”.

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi ƙarƙashin sashe na 147 da 148 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (da aka yi wa gyara).

Shugaba Tinubu ya gode wa ministocin da suka bar mukaman nasu bisa hidimarsu ga ƙasa, tare da yi musu fatan alheri a gaba, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da yin gyare-gyare domin ƙarfafa aikin gwamnati.

MAJIYA:Nigeria Presidency