| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Real Madrid ta sanya fam miliyan 137 kan Vinicius Junior
Vinicius ya kasance ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan Real Madrid a cikin shekarun baya-bayan nan, inda ya zura kwallaye 128 tare da bayar da taimako aka ci ƙwallaye 100 a wasanni 375 da ya buga a dukkan gasa.
Real Madrid ta sanya fam miliyan 137 kan Vinicius Junior
Vinicius zai zama babban kamu ga Arsenal, amma ƙungiyar ta Premier League za ta buƙaci kashe kuɗi mafi yawa a tarihinta


Real Madrid ta tsuga kuɗi kan ɗanwasanta Vinicius Junior wanda ake dangantawa da komawa Arsenal, a cewar jaridar Sport.

Rahoton ya ce shugaban Real Madrid, Florentino Perez, ba zai amince da sayar da ɗan wasan na Brazil ba sai idan wata ƙungiya ta gabatar da tayin da ya kai fam miliyan 137.

Vinicius ya kasance ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan Real Madrid a cikin shekarun baya-bayan nan, inda ya zura kwallaye 128 tare da bayar da taimako aka ci ƙwallaye 100 a wasanni 375 da ya buga a dukkan gasa.

Kwantiragin ɗanwasan a filin wasa na Santiago Bernabeu za ta ƙare a shekara mai zuwa. Sai dai tattaunawar sabunta kwantiraginsa ta tsaya cik, lamarin da ke barin Real Madrid cikin haɗarin rasa shi kyauta a bazara mai zuwa.

Duk da raunin da ƙungiyar ke da shi a tattaunawa kan kwantiragin, rahoton ya ce ƙungiyar ta La Liga ba za ta amince da sayar da Vinicius ba sai an gabatar mata da tayin da ya kai fam miliyan 137.

Arsenal ta riga ta ɗauki Christos Tzolis, amma har yanzu tana neman ƙarin ɗanwasan gaba.

Ana sa ran Gabriel Jesus da Gabriel Martinelli za su bar ƙungiyar a wannan bazarar, abin da ya sa Arsenal ke neman fitaccen ɗan wasan gaba.

Vinicius zai zama babban kamu ga Arsenal, amma ƙungiyar ta Premier League za ta buƙaci kashe kuɗi mafi yawa a tarihinta domin samun sa hannunsa.

Ɗan wasan mai shekaru 26 ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan gaba a duniya, saboda saurinsa, ƙwarewarsa wajen wuce 'yan wasa da kuma iya zura ƙwallaye.

Ya kuma taka rawa sosai a gasar Kofin Duniya da aka gudanar a wannan bazarar, inda ya zura ƙwallaye huɗu a wasanni biyar da ya buga wa Brazil.

 

 

Rumbun Labarai
Ronaldo zai iya komawa tawagar Portugal idan yana so, in ji kocin ƙasar
Tirkashi: Real Madrid na so a ƙwace wa Barcelona kofuna 9, ta gabatar da ƙorafi mai shafi 50,000
Shugaban hukumar ƙwallo da kocin Portugal sun zauna don lallashin Ronaldo bayan ƙin saka shi a wasa
Barcelona ta fusata da Ancelotti kan raunin da Raphinha ya samu a wasan Brazil da Australia
An samu Manchester City da laifin keta dokokin kuɗi
Nijeriya da Ghana sun sha kashi a wasannin neman gurbin shiga Gasar AFCON ta 2027
Manyan kulob sun shirya wawason 'yanwasan Man City idan kotu ta kore ta daga Gasar Firimiya
Zidane ya yaba wa Turkiyya gabannin wasansa na farko a matsayin mai horar da tawagar Faransa
Taiwo ya maye gurbin Osimhen yayin da aka buɗe sansanin horaswa na Super Eagles
Kocin Super Eagles ya fitar da sunayen ‘yanwasan da za su buga wasanni a Satumba da Oktoba
Messi ya ci ƙwallonsa ta 100 a Inter Miami yayin da suka lashe Kofin Campeones
Mbappe ya ce ya ƙi sa rigar Ceuta yadda ya kamata ne don tausaya wa baƙin haure 'yan Morocco
Messi na shirin buga wa Argentina wasansa na ƙarshe
Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara
Falconets ta Nijeriya ta lallasa New Caledonia da ci 10-1, ta kai zagayen gaba a gasar Kofin Duniya
'A Maroko za a yi wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2030', in ji shugaban hukumar ƙwallon kasar
'An yi wa Arsenal fasha a wasansu da Aston Villa', in ji hukumar gasar Firimiya
NFF ta naɗa Eguavoen a matsayin kocin wucin-gadi na Super Falcons
An manta da Raphinha da Pedri cikin 'yanwasa 30 da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or
Barcelona ta miƙa ƙoƙon-bara wajen masu zuba jari don neman kuɗin gyaran filin wasa