| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
ICPC ta miƙa filin ginin gidaje 962 na aikin dala miliyan 65 ga Bankin Lamunin Gidaje na Nijeriya
ICPC ta ce an karɓi rancen dala miliyan 65 inda aka sayi filin domin aiwatar da aikin gina gidaje da bankin ya ƙaddamar a shekarar 2012.
ICPC ta miƙa filin ginin gidaje 962 na aikin dala miliyan 65 ga Bankin Lamunin Gidaje na Nijeriya
A ranar 11 ga Disamba, 2025, Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin ƙwace filaye biyu da ke gundumar Kaba har abada

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaƙa ICPC ta miƙa wani fili da kotu ta ƙwace a Abuja ga Bankin Lamunin Gidaje na Tarayyar Nijeriya (FMBN), bayan Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin ƙwace filin har abada.

An gudanar da bikin miƙa filin ne a ranar Talata a wurin rukunin gidajen Goodluck Jonathan da ke gundumar Kaba a Abuja, inda Shugaban ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu, ya miƙa kadarar ga Manajan Daraktan FMBN, Shehu Usman Osidi.

A cewar hukumar yaƙi da cin hancin, an sayen filin ne tun asali domin wani aikin gina gidaje da bankin ya ƙaddamar a shekarar 2012. An karɓi rancen dala miliyan 65 domin aiwatar da aikin, wanda ake sa ran zai samar da gidaje 962 a kan fili mai kusan kadada 28.

Sai dai ICPC ta ce bincikenta ya nuna cewa an karkatar da kuɗaɗen rancen ba bisa ƙa'ida ba, kuma ba a gina ko gida ɗaya ba. Ta ƙara da cewa an zuba wasu daga cikin kuɗaɗen ta hannun ofisoshin canjin kuɗi tare da fitar da su zuwa ƙasashen waje.

Daga nan ne hukumar ta shigar da ƙarar da ta shafi ɓangaren farar-hula da ta gwamnati. Yayin da aka kammala shari'ar farar-hular, ana ci gaba da sauraron shari'ar laifin.

A ranar 11 ga Disamba, 2025, Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarnin ƙwace filaye biyu da ke gundumar Kaba har abada, bayan ta yanke hukuncin cewa ana zargin kadarorin sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka. Kotun ta kuma umarci ICPC da ta miƙa kadarorin ga FMBN, wanda ta bayyana a matsayin wanda abin ya shafa a shari'ar.

Kotun ta kuma umarci ICPC da FMBN su haɗa kai wajen sa ido kan gina gidaje 962 da aka tsara, tare da tabbatar da cewa an bai wa waɗanda aka tanada wa gidajen. Za a kafa kwamitin sa ido na haɗin gwiwa da ya ƙunshi jami'ai daga ICPC da FMBN domin kula da aiwatar da aikin.

Da yake jawabi yayin bikin miƙa filin, Shugaban ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu, ya ce kwato kadarorin gwamnati na da amfani ne kawai idan an mayar da su ga ayyukan da za su amfanar da al'umma, yana mai ƙarawa da cewa hukumar na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

A nasa jawabin, Manajan Daraktan FMBN, Shehu Usman Osidi, ya yaba wa ICPC bisa nasarar kwato filin, yana mai bayyana matakin a matsayin babban ci gaba wajen kare kadarorin jama'a da tabbatar da cewa sun amfani 'yan Nijeriya kamar yadda aka tsara tun farko.