Saudiyya ta matsa wa Amurka lamba kan ta kawo karshen rufe Mashigar Hormuz da kuma komawa tattaunawa da Iran, a cewar wani rahoto da Jaridar The Wall Street Journal ta fitar a ranar Talata.
Matakin rufe mashigar, wadda Donald Trump ya sanar ta fara aiki da misalin karfe 14:00 na agogon GMT ranar Litinin bayan da tattaunawa tsakanin Washington da Tehran ta rushe a karshen mako a Islamabad.
Yarjejeniyar tattaunawar wani bangare ne na kokarin da ake yi na dakatar da faɗan da ya shafi Iran, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a yankin tun daga karshen watan Fabrairu.
Riyadh ta kara nuna damuwa kan cewa matakin zai iya haifar da ramuwar gayya daga Iran fiye da batun Mashigar Hormuz, musamman ma kan Bab al Mandeb, wata hanya da ke da matukar muhimmanci wajen fitar da mai daga Saudiyya.
"Kasashen yankin Gulf ba sa son yaƙin tare da barin ikon Mashigar Hormuz a hannun Iran," in ji rahoton, yana mai nuni kan babban kalubale da ke gaban tattalin arzikin yankin wanda ya dogara kan jigilar makamashi.
Duk da matakai masu tsauri da ke fitowa daga Washington da Tehran, rahoton ya ce bangarorin biyu suna ci gaba da tattaunawa ta hanyar masu shiga tsakani kuma a shirye suke su ci gaba da tattaunawa idan yanayi ya ba da dama.
A yanzu haka dai, Saudiyya da sauran ƙasashen yankin Gulf suna fafutukar farfaɗo da diflomasiyya, suna masu fatan hana katse wasu ƙarin hanyoyin mai na duniya da kuma guje wa faɗaɗa rikici a yankin.






