| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
NAHCON ta ba da umarnin bincike kan wani abinci da mahajjata suka ƙi ci kan 'rashin inganci'
Sanarwar ta ce wasu daga cikin abincin dare da aka bayar a ranar 27 ga Mayun 2026 ba su cika ƙa’idojin da suka shafi sarrafawa da mazubinsa ba, saboda haka aka yi watsi da su nan take tare da haɗin gwiwar jami’an NAHCON.
NAHCON ta ba da umarnin bincike kan wani abinci da mahajjata suka ƙi ci kan 'rashin inganci'
NAHCON ta ba da umarnin bincike kan wani abinci da mahajjata suka ƙi ci kan 'rashin inganci' / Others

Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da bin tsauraran ƙa’idojin ingancin abinci yayin Aikin Hajjin 2026 da ake gudanarwa, bayan da mahajjata suka ƙi cin wani abincin dare da aka tanadar wa mahajjatan Nijeriya a Saudiyya.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, NAHCON ta bayyana cewa hukumomin lafiya na Saudiyya na ci gaba da aiwatar da tsauraran matakan imganta abinci domin tabbatar da jin daɗin dukkan mahajjata, musamman la’akari da yanayin zafi da ake fama da shi a ƙasar.

Sanarwar ta ce wasu daga cikin abincin dare da aka bayar a ranar 27 ga Mayun 2026 ba su cika ƙa’idojin da suka shafi sarrafawa da mazubinsa ba, saboda haka aka yi watsi da su nan take tare da haɗin gwiwar jami’an NAHCON.

Domin rage tasirin lamarin ga mahajjatan da abin ya shafa, kamfanin da ke kula da hidimar abinci ya samar da wasu kayan ƙwalam na wucin gadi, yayin da mambobin hukumar NAHCON suka zagaya domin yi wa jami’an jihohi bayani tare da kwantar musu da hankali.

Shugaban hukumar NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya umarci Kwamitin Tsaro na hukumar da ya gudanar da bincike kan masu samar da abincin da kuma waɗanda suka taimaka wajen ba su kwangilar.

A wani ci gaban kuma, shugaban ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan wasu masu gudanar da yawon Hajji da ake zargi da shigo da mahajjata fiye da adadin da suka yi rajista da kuma cin zarafin wasu mahajjata marasa laifi.

NAHCON ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifi bayan kammala bincike zai fuskanci hukunci, ciki har da soke lasisin gudanar da ayyukansa.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an fara shirye-shiryen mayar wa mahajjatan da lamarin ya shafa kuɗinsu cikin gaggawa.

NAHCON ta gode wa mahajjatan Nijeriya bisa fahimta da haƙurin da suka nuna, tare da sake tabbatar da jajircewarta wajen kula da walwala, lafiya da jin daɗinsu a duk tsawon lokacin aikin Hajji.