Damuwa kan kutsawar 'yan bindiga Jihar Kano
Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Nijeriya waɗanda ake da zaman lafiya da kwanciyar hankali, idan aka kwatanta da sauran yankin da matsalar tsaro ta yi ƙamari.
Ana nuna fargaba da damuwa dangane da yadda ake ci gaba da samun rahotannin kashe-kashe da sace-sacen mutane domin neman kuɗin fansa da kuma aikace-aikacen ’yan bindiga a wasu sassan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya.
Jihar Kano na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Nijeriya waɗanda ake da zaman lafiya da kwanciyar hankali, idan aka kwatanta da sauran yankin da matsalar tsaro ta yi ƙamari.
Jihohin arewacin ƙasar kamar Zamfara da Kaduna da Katsina su ne matsalar tsaro ta fi ƙamari kuma masana harkokin tsaro suna ganin cewa kasancewar Jihar Kano ta yi maƙwabtaka da jihohin Katsina da Kaduna hakan ne ya jefa ta cikin barazanar kwararar ’yan bindigar da suka addabi maƙwabtan nata.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa matsalar tsaro ta ’yan bindiga da ake fuskanta yanzu tana faruwa ne a wasu ƙauyuka da ke Ƙananan Hukumomin Tsanyawa da Shanono, waɗanda suke da iyaka da Jihar Katsina.
SP Kiyawa ya ce jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu wajen daƙile wannan babbar barazana, sannan zuwa yanzu sun kama mutum uku waɗanda ake zargi, kuma suna faɗaɗa bincike a kansu.
Ya ce rundunar ’yan sanda sun yi nasarar kama mutanen da ake zargin ’yan bindiga ne masu satar mutane a ƙarshen watan jiya, bayan samun wasu bayanan sirri.
Sannan idan za a tuna a makon jiya ne rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kashe ’yan bindiga 19 a jihar, yayin artabu da dakarunta suka yi da su kuma sakamakon haka sojoji biyu sun mutu da wani ɗan sa-kai guda ɗaya, kamar yadda mai magana da yawun rundunar Babatunde Zubairu ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.
Sojojin sun kai farmaki ne wata maɓoyar ’yan bindigar a Ƙaramar Hukumar Shanono tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaron ƙasar.
Kazalika Shugaban kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Nijeriya kuma masani kan al’amuran da suka shafi tsaro Dakta Kabiru Adamu ya ce dalilai da dama ne suka jawo ɓullar matsalar tsaro Jihar Kano, ciki har da wasu matakai da wasu jihohi maƙwabtanta suke ɗauka kamar matakin sulhu da aka yi da su a Jihar Katsina.
Masanin ya ce wajibi ne hukumomi su tashi tsaye wajen yaƙi da wannan matsala saboda yadda take gurgunta rayuwar al’umma gaba ɗaya, kuma ya ce Kano jiha ce mai mahimmancin gaske ga arewacin Nijeriya, wanda ya ce idan wannan matsala ta mamaye ta, to matsalar za ta iya shafar gaba ɗaya arewa.
Dakta Kabiru Adamu ya ce duk da cewa gwamnatin jihar tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar, akwai buƙatar ta samar da wani tsarin musamman na matakan tsaro irin wanda ake da shi a wasu jihohin ƙasar kamar Jihar Legas.
Ya ce saboda girman Jihar Kano da kuma muhimmancinta, kamata ya yi gwamnan Kano ya kafa matakan tabbatar da tsaro a matakin al’ummomi cikinsu har da samar da hanyar gano matsalar tsaro da wuri tun kafin abin ya zama babbar matsala.
Ya ce tsarin zai haɗa da samar da wasu lambobin gaggawa da kowane mazaunin Kano idan yana cikin matsala zai iya kiran jami’an tsaro a koyaushe, kuma jami’an tsaron su kai masa ɗauki a cikin mintuna bakwai zuwa 15 a ko ina yake a cikin jihar. Ya ce ta haka ne za a iya dakile wannan matsala tun daga tushe.