Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Bayan mayaƙan RSF sun ƙwace Al Fasher, sun mayar da hankali wurin yin arangama da sojojin Sudan a wasu sabbin wurare.
Sojojin Sudan ranar Alhamis sun daƙile wani hari na jirgi maras matuƙi da mayaƙan Rapid Support Forces (RSF) suka kai a wasu mahimman wurare, ciki har da filin jirgin sama da wata madatasar ruwa a arewacin ƙasar.
Runduna ta 19 ta sojojin ƙasar ta bayyana a wata sanarwa cewa dakarunta sun daƙile wasu jirage marasa matuƙa na ƙunar-baƙin-wake da RSF ta tura da safiyar Alhamis a wani yunƙuri na kai hari a hedkwatar rundunar da filin jiragen sama na Merowe da kuma dam ɗin Merowe a jihar ta Northern State.
An ji ƙarar ababe masu fashewa a harabar filin jiragen saman da dam ɗin, kamar yadda shaidu suka bayyana wa kafar yada labaram Sudan News ta ƙasar. Ba a dai gane iyakar ɓarnar da harin ya yi ba.
Babu wani tsokaci nan take daga rundunar RSF game da sanarwar da sojin ƙasar ta fitar.
A matsayin ɗaya daga cikin mahimman wurare a arewacin Sudan, Merowe ya ƙunshi wani filin jiragen sama da ake amfani da shi domin buƙatu na soji da na fararen-hula tare da dam ɗin Merowe, ɗaya daga cikin ababen more rayuwa da suka fi girma a ƙasar.
Al-Rakoba News, wadda ta ambato majiyoyi na cikin gida, ta ce harin ya kuma mayar da hankali kan babban birnin Jihar Dongola da kuma birnin Al-Dabba.
Bayan RSF ta ƙwace Al Fasher, babban birnin Jihar North Darfur, arangama tsakanin ƙungiyar da sojin Sudan ta bazu zuwa sabbin wuraren yaƙi, musamman jihohin tsakiya da kudancin Kordofan.
Daga cikin jihohin Sudan 18, a halin yanzu rundunar RSF tana riƙe da dukkan jihohi biyar na yankin Darfur, face wasu yankunan arewaci kaɗan na North Darfur wadanda har yanzu ke ƙarƙashin ikon soji.
Sojin Sudan na ci gaba da mamaye yawancin sauran jihohi 13 a yankunan kudanci da arewa da gabashi da kuma tsakiya ciki har da babban birnin ƙasar Khartoum.
Rikicin na zub da jini tsakanin soji da RSF, wanda aka fara a watan Afrilun shekarar 2023, ya kashe dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da gidajensu.