Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya bayar da tabbacin cewa Iran za ta halarci gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026, duk da yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra’ila da kuma Tehran.
“Shakka babu Iran za ta zo. Muna fatan cewa kafin lokacin a samu zaman lafiya, wanda hakan tabbas zai taimaka,” in ji Infantino a yayin tattaunawa da gidan talbijin na CNBC.
“Amma dole ne Iran ta zo, suna wakiltar mutanensu ne, sun cancanta, kuma ’yanwasan suna son yin wasa,” in ji shi game da wasannin tawagar ƙasar da aka shirya yi a Amurka a watan Yuni.
Ya ƙara da cewa “ya kamata a raba harkokin wasanni da siyasa.”
“Idan babu wanda ya yi imanin haɗa kan mutane da tabbatar da ɗorewar hakan, to mu muna gudanar da wannan aikin,” in ji shi.
Waɗannan kalaman sun zo ne bayan da Mexico ta tabbatar da cewa FIFA ta ƙi amincewa da buƙatar Iran ta mayar da dukkan wasanninta zuwa maƙociyar Amurka.
Shakkun Shiga Gasar
An shiga fargaba game da shigar Iran gasar ta duniya sakamakon yaƙin da ya ɓarke tsakaninta da Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu.
Iran ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta shekarar 2026 ne a watan Maris na 2025 bayan sun tashi kunnen doki 2-2 da Uzbekistan.
Gasar cin kofin duniyar, wadda Amurka, Mexico, da Canada suke karɓar baƙunci tare, za ta fara ne a ranar 11 ga watan Yuni.
Sai dai, an tsara cewa Iran za ta buga dukkan wasanninta na rukunin G — wanda ya haɗa da Belgium, Masar da New Zealand — a cikin ƙasar Amurka.
Bisa ga jadawalin wasannin tawagar da ke kan shafin yanar gizon FIFA, an shirya Iran za ta fafata da New Zealand a ranar 15 ga Yuni a filin wasa na Los Angeles, sannan ta kara da Belgium a ranar 21 ga Yuni a wannan filin, sannan ta fafata da Masar a ranar 26 ga Yuni a filin wasa na Seattle.
WASANNI
2 minti karatu
Shugaban FIFA ya ce akwai ‘tabbacin’ Iran za ta halarci Gasar Cin Kofin Duniya
Wannan bayani na zuwa ne bayan da mahukunta a Mexico sun tabbatar da cewa FIFA ta yi watsi da buƙatar Iran ta mayar da dukkan wasanninta zuwa ƙasar ta Mexico.
Rumbun Labarai





