Malawi za ta bi sahun wasu ƙasashe wajen dawo da 'yan ƙasarta da ke neman barin Afirka ta Kudu, inda ake ta samun rahotannin hare-haren da ake kai wa 'yan Afirka da suke wasu sassan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren ranar Talata, Ma'aikatar Harkokin Wajen Malawi ta ce za a takaita shirin ga 'yan ƙasar da suka nemi su dawo ƙasarsu ta asali, kana ta sanar da fitar da cikakkun bayanai da zarar an kammala shirye-shiryen tafiyar.
Hare-haren ƙyamar baƙi sun zama wata babbar matsala da ake ci gaba da fuskanta a Afirka ta Kudu, inda galibi ake zargin baƙi da janyo ƙalubale na tattalin arziki cikin har da rashin aikin yi.
Ƙungiyoyin da ke adawa da baƙi sun sanya wa'adin ranar 30 ga Yuni ga baƙi marasa takardu su bar ƙasar, wanda hakan ya ƙara yawan fargaba a tsakanin al'ummomin 'yan ci-rani.
Mozambique ta ce an kashe 'yan ƙasarta biyar a tashin hankalin da ya faru a garin Mossel Bay da ke yankin bakin teku a ƙarshen mako, yayin da Ghana ta mayar da ɗaruruwan 'yan ƙasarta a makon da ya gabata.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi alƙawarin ɗaukar mataki kan waɗanda ke irin wannan aika-aika ko kuma suke far wa 'yan ci-rani.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya shaida wa majalisar dokoki na ƙasar a ranar Talata cewa duk da magance matsalar kwararar baƙin haure yana da muhimmanci, bai kamata kasar ta rikiɗe zuwa wani "tashin hankali, da kyamar baƙi da kuma tsangwama ba."
Afirka ta Kudu tana da tattalin arziki mafi girma a nahiyar kuma wuri ne da mutane daga ƙasashe makwabta ke zuwa neman aiki. Haka kuma tana karɓar 'yan gudun hijira da masu neman mafaka da ke tserewa daga rikici a ƙasashe kamar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

















