Za a gurfanar da wasu sojojin Nijeriya a gaban kotun soji kan yunƙurin kifar da gwamnati

Manjo Janar Samaila Uba ya ce rundunar sojin ta Nijeriya za ta ɗauki matakin ne a matsayin hukunci tare da ƙoƙarin bin ƙa’ida.

By
Sanarwar ta ce binciken da aka gudanar ya yi nazari kan mutanen da suke da hannu a lamarin. / AA

Rundunar sojin Nijeriya ta ce za ta gurfanar da wasu jami’anta a gaban kotun soji domin fuskantar tuhuma kan zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai na Hedkwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Samaila Uba ya fitar ranar Litinin ta ce za a tuhumi sojojin ne kamar yadda dokar soji da sauran dokokin ƙasar suna tanada.

Sanarwar ta ce, “idan ba a manta ba Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta fitar da wata sanarwa a watan Oktoban 2025 game da kama sojoji goma sha shida kan rashin ɗa’a da keta dokokin aiki. Rundunar Sojin Nijeriya tana mai shaida wa al’umma cewa an kammala bincike kuma an miƙa rahoto ga manyan jami’a kamar yadda doka ta buƙata.

“ Cikakken binciken da aka gudanar bisa tanade-tanaden soji, ya yi nazari cikin tsanaki kan dukkan batutuwa da suka jiɓanci mutanen da suke da hannu a lamarin.

“Binciken ya gano wasu sojoji da ake zargi sun yi yunƙurin kifar da gwamnati lamarin da ya saɓa wa dokoki da tsari da ake buƙata daga mambobin rundunar sojin Nijeriya.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “sojojin da ke da alamar tambaya a kansu za su gurfana a gaban kotun soji domin fuskantar tuhuma kamar yadda dokokin soji da sauran dokoki suna tanada.”

Manjo Janar Samaila Uba ya ce rundunar sojin ta Nijeriya za ta ɗauki matakin ne a matsayin hukunci tare da ƙoƙarin bin ƙa’ida.