| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Majalisar Wakilan Nijeriya ta amince da ƙudurorin sauya dokar haraji
A ranar Alhamis ne Majalisar Wakilan ta amince da rahotan ƙudurorin gyara haraji guda hudu a zamanta da ta yi a Abuja, kamar yadda mai taimaka wa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Watsa Labarai ya wallafa a shafinsa na X.
Majalisar Wakilan Nijeriya ta amince da ƙudurorin sauya dokar haraji
Tajudden Abbas / Others

Majalisar Wakilan Nijeriya ta amince da kudirin sake fasalin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya miƙa wa majalisar dokokin kasar.

A ranar Alhamis ne Majalisar Wakilan ta amince da rahotan ƙudurorin gyara haraji guda hudu a zamanta da ta yi a Abuja, kamar yadda mai taimaka wa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Watsa Labarai ya wallafa a shafinsa na X.

A yanzu ana jiran amincewar Majalisar Dattijai ne.

Kudurorin sun hada da dokar harajin Nijeriya da daftarin kula da haraji da dokar hukumar haraji, da kuma dokar kafa hukumar tattara kudaden shiga ta Nijeriya.

Wannan ya biyo bayan nazarin saɗara-saɗara na duk gyare-gyaren da suka dace akan kudurorin a Kwamitin Gabaɗaya.

Wasu daga cikin gyare-gyaren sun haɗa da barin harajin VAT a kan yadda yake a yanzu wato kashi 7.5 cikin 100, sabanin yadda aka so ƙara shi, da kuma tsawaita keɓance harajin kuɗin shiga ga takamaiman kasuwancin noma da jami'an soja.

Tare da amincewa da rahoton kan kudurorin haraji, Majalisar Wakilai na kokarin ganin ta amince da kudirin haraji a mako mai zuwa yadda zai zama doka.

Tsarin raba kuɗaɗen haraji na VAT da majalisar ta amince da shi:

Za a dinga raba kashi 50 cikin 100 daidai wa daida ga jihohin ƙasar

Sai kuma a raba kashi 20 cikin 100 bisa ga yawan jama’ar jihohi

Kashi 30 cikin 100 kuma za a raba shi bisa ga abin da yawan abin da jihohin ke samarwa

Kawar da damuwowin ‘yan Nijeriya

Da yake jawabi bayan majalisar ta yi nazari tare da amincewa da rahotan kudirorin gyara haraji guda hudu, Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Wakilai, James Faleke, ya bayyana cewa an kawar da dukkan damuwar da ‘yan Nijeriya suka nuna a cikin takardun.

Dan majalisar ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa dokar sake fasalin haraji za ta samar da dokokin da za su samu karbuwa sosai.

“An shafe kwanaki uku ana zaman sauraron ra’ayoyin jama’a a kan waɗannan ƙudurorin, tare da gabatar da bayanai daga manyan masu ruwa da tsaki sama da 80. Bayan haka, mun gudanar da ganawa ta kwanaki takwas don yin muhawara a kan kowace saɗara.

"Na yi farin ciki da cewa 'yan majalisar sun amince da kyakkyawan aikinmu kuma sun amince da duk shawarwarinmu," in ji Faleke.

Majalisar ta yi gyaran fuska ga batun harajin gado mai cike da cece-kuce, inda ta bayyana cewa duk wani gadon da aka samu kafin rushe batun ba za a iya biya masa haraji ba.

Majalisar ta kuma amince da samar da ci gaba da ba da tallafi ga hukumomin TETFUND, NASENI, da NITDA ta hanyar asusun ci gaba.

Rumbun Labarai
An kai hari kan ayarin motocin Peter Obi na Jam'iyyar NDC a Jihar Cross River
'Yansanda sun kama mutum 103 da ƙwayoyi da makamai a jihar Borno ta Nijeriya
Rundunar ’yansandan Nijeriya ta gargaɗi ’yan siyasa kan lalata kayan kamfen gabanin zaɓen 2027
EFCC ta bankaɗo haramtacciyar matatar mai da ake zargin ’yan China suna gudanarwa a Jihar Ogun
'Yansanda sun bankaɗo wurin buga jabun daloli, sun kama mutum ɗaya a Ondo
Asusun gwamnatin Tarayyar Nijeriya na N10b ba na cutar Ebola kaɗai ba ne, in ji shugaban NCDC
Gwamnatin Nijeriya ta kama wasu da ake zargi da aikin rajistar lambar NIN ba bisa ƙa'ida ba
Sojojin Nijeriya sun kashe manyan Shugabannin Daesh a Borno
’Yanbindiga sun sace kimanin yara 12 a Jihar Neja
Gwaji ya tabbatar mutum biyu da ake zargin suna ɗauke da Ebola a Adamawa ba su da cutar - NCDC
’Yansanda sun dakile harin ‘yanta'adda a Zamfara, sun gano gawarwaki fiye da 30
An gano mutum biyu da ake zargin sun kamu da cutar Ebola a Arewa maso Gabashin Nijeriya
INEC ta wallafa sunan Pantami a shafinta na ’yantakarar gwamna amma babu Gwarzo na Kano
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da shirin tallafin kuɗi na N50,000 ga ’yan ƙasar da ke cikin talauci
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda Daesh 48, sun ƙwato makamai a jihohin Borno da Yobe
Wani sufeton ‘yansanda da fararen-hula 11 sun rasa rayukansu a wasu hare-haren ta’addanci a Kebbi
Tinubu ya kare matakin karɓo bashi daga waje, ya ce Nijeriya na buƙatar haɓaka tattalin arziki
NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu da haramta amfani da su na Naira Biliyan 8 a Jihar Nasarawa
Dakarun Nijeriya sun ce sun kashe ‘yanta’adda 42 a arewa maso gabashin ƙasar
Nijeriya ta amince da biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya naira 70,000 kudin sufuri duk wata