Duniyoyi shida za su jeru da juna a layi ɗaya a sararin samaniya ranar Asabar

Za a iya ganin duniyoyin Mercury da Venus da Jupiter da Saturn da Uranus da Neptune da ido ƙuru-ƙuru a jere a sararin samaniya jim kaɗan bayan faɗuwar rana.

By
Duniyoyi shida za su jeru da juna a layi ɗaya a sararin samaniya ranar Asabar / Reuters

Za a ga wani al’ajabi na jeruwar duniyoyi shida a layi ɗaya a sararin samaniya a ranar Asabar, wani lamari da ake yawan bayyana shi da “jeren duniyoyi,” a cewar rahotannin masana kimiyyar sararin samaniya.

Ana sa ran duniyoyin Mercury, Venus, Jupiter, Saturn, Uranus da Neptune za su bayyana a layi guda a wani ɓangaren sararin samaniya jim kaɗan bayan faɗuwar rana, inda kallon hakan ta taga zai ɗauki kusan mintuna 30 zuwa 45 kafin wasu daga cikin duniyoyin su ɓace daga maƙurar gani.

Wannan lamari wata jeruwa ce da taurari ke yi a kan layin da suke zagaye rana, abin da aka fi sani da kusufi wato ecliptic. Daga Duniyarmu ta Earth, wannan daidaiton zai iya sanya duniyoyi da yawa su jeru a cikin yanki guda a sararin samaniya a lokaci ɗaya.

Gani da ido ƙuru-ƙuru

Ana sa ran za a iya ganin huɗu daga cikin waɗannan duniyoyi guda shida ba tare da madubin hangen nesa ba.

Tauraruwa Zara da aka sani da Venus da Turanci, za ta bayyana ƙasa-ƙasa a yammacin a sararin samaniya kusa da Burujin Dalwu wato Aquarius kuma zai kasance mafi haske a jerin, yana haskakawa da kusan ƙarfin -3.9.

Za a ga Jupiter a gefen Burujin Jauza wato Gemini a sararin samaniya, yayin da Saturn zai bayyana a tsakaninsu a Burujin Hutu wato Pisces.

Duniyar Mercury za ta kasance kusa da maƙurar gani daga ɓangaren yamma kuma zai yi wahalar gani idan har samaniyar ba ta kasance tarwai ba.

Su kuwa sauran duniyoyin biyu da suka rage ba za su ganu ba sai da madubin hangen nesa.

Neptune, da ke kusa da Saturn, za ta yi dushi-dushi sosai ta yadda ba za ta ganu da ido sosai ba, yayin da ita ma Duniyar Uranus, wacce take a saman Burujin Sauru wato Taurus kusa da taurarin Pleiades da aka fi sani da ‘Yan mata Bakwai da Hausa, za ta yi wahalar ganuwa saboda wata da ya kusan zama cikakken.

Irinsu wannan jeruwa na faruwa ne lokacin da duniyoyi da dama suka cika wani ƙaramin ɓangare na sararin samaniya.

Masana ilimin taurari sun ce wannan jere zai fi sauƙin gani daga saman duniya wato daga Arewaci.