Gwarzo a fagen waƙar Afrobeats Davido ya shiga cikin jerin mawaƙan da za su yi waƙa a gasar Cin Kofin Duniya .
A filayen wasanni na gasar da ke ƙasashen Amurka da Mexico da Kanada, sautin gasar a bayyana yake cewa na Afirka ne.
An zaɓi Davido a matsayin mafi shaharar mawaƙin da zai yi waƙa a bikin buɗe gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA ranar 11 ga watan Yuni a Los Angeles, Amurka.
Inda zai hau dandalin Crypto.com tare da Major Lazer na Diplo, tauraron na Nijeriya na ci gaba da kasancewa a kan gaba a matsayin jakadan duniya na sautin Afrobeats.
A sanarwar da ta fitar ranar 2 ga watan Yuni , FIFA ta ce waƙar bikin buɗe gasar ta Davido za ta kasance "wani biki mai cike da ƙuzari mai yawa" da kuma wani "daren waƙa da ƙwallon ƙafa da al’adu da ba za a iya mancewa da shi ba".
Amma karin sautin Afirkan bai tsaya a nan ba.
Bukukuwan buɗe gasar za su bayyana ƙuzarin matasa ‘yan Gen Z da ya ruɓanya.
Ɗan Afirka ta Kudu da ya lashe kyautar Grammy Tyla zai kasance a dandalin a birnin Mexico City ranar 11 ga watan Yuni, kafin ya haɗa kai da tauraron waƙar Afrobeats Rema washe gari a filin wasan SoFi a Los Angeles a wasan farko na Amurka.
Sai dai kuma, labarin da ya fi daɗi ta yiwu shi ne labarin ƙananan yara na unguwar marasa galihu na Uganda.
Waɗannan matasa masu rawa, waɗanda suka fara tafiyarsu a kan titunan unguwar Katwe na Kampala, sun sami aikin da ba kasafai ake samunsa a rayuwa ba.
Shahararriyar mawaƙiyar duniya Shakira ce ta gayyaci tawagar rawar ta shiga cikin waɗanda za su yi wasa a ranar ƙarshe ta gasar cin kofin duniya a New Jersey, ranar 19 ga watan Juli.
Za su gabatar da "Dai Dai," waƙar gasar da ta ƙunshi tauraron da ya lashe kyautar Grammy Burna Boy. Shakira da burna Boy za su yi waƙa a Mexico City, bukukuwa uku na farko na buɗe gasar.
Daga kan titunan Kampala zuwa ɗaya daga dandamali mafi girma a duniya, wani abu ɗaya a bayyane yake, gasar ƙwallon ƙafa ta duniyar tana zamowa wadda ta fi girma ga Afirka zuwa yanzu.
Nahiyar za ta samu wakilcin tawagogin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 10 a karon farko a tarihin gasar Cin Kofin Duniya.
Senegal da Maroko da Masar da Gahana da Aljeriya da Tunisia da Afirka ta Kudu da Côte d’Ivoire da Cabo Verde da kuma Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo su ne ƙasashen Afirkan da ke cikin gasar.
Yayin da Cabo Verde ke shiga gasar a karon farko a tarihin gasar, DRC za ta koma gasar a karon farko tun shekarar 1974.
Gasar da ke haɗa waƙa da ƙwallon ƙafa wata aba ce da Afirka za ta iya samun abubuwa da dama daga gareta kamar sauran sassan duniya.











