| hausa
KASUWANCI
2 minti karatu
Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko
Ministan Kuɗi na Ghana, Cassiel Ato Forson, wanda ya bayyana matsayin da kwamitin ya ɗauka, ya ce sabon farashin na nufin za a riƙa sayen kowane buhun koko mai nauyin kilogiran 64 kan GH₵3,625.
Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko
Ghana ɗaya ce daga cikin ƙasashen da suka fi noman koko a duniya
3 Oktoba 2025

Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko zuwa GH₵5,800 kan ko wane tan bayan zaman gaggawa da kwamitin da ke sanya farashin ga noman kokon ya yi.

Ministan Kuɗi, Cassin ƙasar Cassiel Ato Forson, wanda ya bayyana matsayin da kwamitin ya ɗauka, ya ce sabon farashin na nufin za a riƙa sayen kowane buhun koko mai nauyin kilogiran 64 kan GH₵3,625.

Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito cewa wannan na nufin an samu ƙarin GH₵4,00 kan ko wane buhun koko.

A watan Agusta na wannan shekarar gwamnatin ƙasar ta ƙayyade farashin da manoma za su sayar da koko a kakar 2025/2026 kan GH₵51,660 kan ko wane tan na koko.

Sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar Jumma’a 3 ga watan Oktoban shekarar 2025.

Dakta Forson ya bayyana cewa farashin na baya ya kasance bisa hasashen da aka yi ne kan farashin koko a duniya da kuma farashin a kasuwar musayar kuɗaɗe ta ƙasa da ƙasa.

“Daga bisani, mun ga wasu sauye-sauye, saboda haka yana da muhimmanci mu sake sauya farashin ga manoma, “ in ji Dakta Forson.

Ya ce hukumar kula da koko ta COCOBOD za ta ci gaba da ɗaukar matakai domin tallafa wa noman koko da kuma inganta rayuwar manoma.

Ya ce COCOBOD za ta ƙara ƙaimi wajen bayar da takin zamani na koko a kyauta (na ruwa da na ƙwaya) da maganin kashe ƙwari da injinan feshi kyauta da sauransu.

Kazalika ya ce hukumar COCOBOD na kan hanyarta ta samar da sabon tsarin karatu kyauta ga ya’yan manoma koko a shekarar karatu ta shekarar 2025/20-26.

Ya ce gwamnatin ta jajirce wajen tallafa wa hukumar koko ta Ghana wajen gina fannin ta yadda duk masu ruwa da tsaki za su amfana.

 

Rumbun Labarai
Kamfanin simintin Dangote ya fara aiki a ƙasar Ivory Coast
Ana hasashen mambobin OPEC+ za su ƙara yawan fetur ɗin da suke fitarwa yayin da farashinsa ke karewa
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta makamashi da tattalin arziki
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai tiriliyan a duniya: rahoto
Dangote zai mai da ma'aikatan Matatar Mai da aka kora daga aiki - Ma'aikatar Ƙwadagon Nijeriya
Kamfanin Orano na Faransa ya ce ya tara tan 1,500 na uranium a Nijar
Kamfanonin haɗin gwiwa ƙarƙashin Saudiyya za su sayi kamfanin wasannin game na Electronic Arts (EA)
Kamfanin Turkish Airlines zai sayi jiragen sama na Boeing 225 bayan Trump da Erdogan sun tattauna
Hukumomi a Ghana sun kama mutanen da ake zargi da yin fasa-ƙwaurin zinari
Matatar mai ta Dangote ta yi watsi da jita-jitar dakatar da aiki na wasu watanni
Babban Bankin Ghana ya dakatar da lasisin cinikin kuɗin ƙetare na UBA da wasu manhajojin aika kuɗi
Farashin ƙwallon kaɗanya ya faɗi warwas a Nijeriya bayan ƙasar ta dakatar da fitar da shi
Babban Bankin Ghana ya ba da sabbin sharuɗɗan kuɗaɗen ƙetare ga masu shiga da kayayyaki
Madogarar bincike kan abincin da aka sauya wa halitta (GMO), da dalilan karɓuwarsa a Nijeriya
Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD
Nijeriya na sa ran ganin sakamako mai kyau bayan aiwatar da wani kyakkyawan tsari a harkar kamfanoni
Kamfanin Tsaro na Turkiyya zai ƙulla yarjejeniya da Malaysia don samar mata da motocin yaƙi
Turkiyya da Libya sun kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai, samar da makamashi da ababen more rayuwa
Filin jiragen sama na Istanbul ya sake cirar tutar tashin jirage a Turai, in ji Ministan Sufuri
China da Amurka sun cim ma yarjejeniyar kasuwanci