Shugaban ƙasar Zambia Hakainde Hichilema ya halarci bikin Kuomboka na ƙasar, tare da shugabannin gargajiya da kuma dubban ‘yan kallo a cikin wani gagarumin yanayi na bayyana kayan tarihi na al'adu.
Taron bikin wadda ake gudanarwa duk shekara a lardin yankin yammacin Zambia al'ada ce da ta ɗauki tsawon shekaru 300 ana yi.
Bikin 'Kuomboka' na Zambia yana nuna ƙarshen lokacin damina da kuma komawar Sarki ko 'Litunga' na al'ummar Lozi zuwa kan tsauni bayan ambaliyar ruwa ta bazara.
Yayin da Kogin Zambezi ya mamaye ƙasar Barotse na Zambia, Kuomboka - na nufin "koma wa daga damina zuwa bazara" - ya kankama.
Shugaba Hichilema ya isa yankin Mongu a ranar Asabar, 28 ga Maris, kana sai ya wuce ƙauyen masautar Lealui, gidan Sarki Lubosi Imwiko na II na lokacin rani.
‘Alamar sarauta’
Jigon abin da ya fi daukar hankali a bikin shi ne tafiyar Litunga a cikin kwale-kwalen sarauta, wanda aka fi sani da Nalikwanda, tun daga Lealui zuwa Barotse Plain da ruwa ya mamaye har tsaunin Limulunga. Sannan ya dawo a watan Agusta.
Kwale-kwalen yana dauƙe da matuƙa mutum 80 zuwa 100, yayin da wasu mutanen ke buga ganguna na sarautar Maoma, suna waƙa, da rawa.
Soma buga ganga na nuna shirin Litunga na barin wurin da ambaliyar ruwa ya fi yawa.
Nalikwanda na ɗauke da wani babban giwa da aka sassaka da ke nuna- alama ta sarauta.
Yayin da kwale-kwalen ke tafiya gaba, mutanen da ke cikinsa za su kunna wuta don nuna wa masu kallo cewa sarkin yana cikin jirgin kuma yana cikin koshin lafiya
Kwale-kwale na biyu kuwa, wato Nalwange ko egret, yana ɗauke da sarauniya, wacce fikafikan tsuntsayenta ke kaɗawa yayin da jirgin ke tafiya.
Bikin al'adu
Wani abin alfahari ne a zaɓe mutum a matsayin mai tuka kwale-kwalen ko kuma tawagar masu sarrafa Nalikwanda, inda gabaki daya suke sanya ja-jayen hukuna.
Sarki Lubosi Imwiko II, Wanda ke rike da mulki tun daga watan Oktoba na 2000, yana a matsayin mai kula da gadon mutanen Lozi.
Shugaba Hichilema ya bayyana "nasarar" bikin, inda ya yi ƙari da cewa al'adu da tarihin al’ummar sun kasance "mabuɗin haɓaka haɗin kan ƙasa."
A yayin bikin, Shugaban Zambia da Sarki Imwiko na II sun saka kayan gargajiya, ciki har da Siziba, kayan a’adu na Lozi mai launin ja da aka yi da yadin chitenge
A ‘yan kwanakin nan kayan gargajiya na Siziba ta jawo hankalin jama'a a shafukan sada zumunta a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce tsakanin 'yan Ghana da 'yan Zambia bayan da shugaban Ghana John Mahama ya sanya kayan kwalliyar fugu na Ghana a lokacin ziyararsa a Lusaka a watan Fabrairun 2026.
Wasu 'yan Zambia cikin barkwanci sun bayyana kayan gargajiya ta fugu na Ghana da ‘‘rigar mata,’’wanda hakan ya sa 'yan Ghana, ciki har da jami'ai, suka riga bayyana fugu wa duniya, yayin da 'yan Zambia kuma suka nuna Siziba.











