| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Iran ta harbo jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35
Rundunar IRGC ta yi iƙirarin cewa ta lalata jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 na biyu yayin da tashin hankali ke ƙaruwa kuma hare-haren soji ke ci gaba a faɗin Gabas ta Tsakiya.
Iran ta harbo jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35
Iran ta yi iƙirarin harbo jirgin yaƙin Amurka samfurin US F-35 yayin da tashin hankali ke ƙaruwa . [TSOHON HOTO] / Reuters / Reuters
4 awanni baya

Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta yi iƙirarin cewa ta harbo wani jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 a yankin tsakiyar ƙasar, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar Iran suka ruwaito.

Sakamakon lalata jirgin, ba a san halin da matuƙinsa yake ciki ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Tasnim News Agency na Iran ya ruwaito, inda ya ambato wata sanarwa da rundunar IRGC ta fitar.

Iƙirarin shi ne karo da biyu da Iran take cewa ta harbo wani jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 yayin ƙarin taɓarɓarewar lamura da ake samu tun da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da yaƙin kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu.

Amurka ba ta mayar da martani game rahoton ba kawo yanzu.

Masu AlakaTRT Afrika - Iran ta ce Mashigar Teku ta Hormuz a bude take ga duniya, amma a rufe ga maƙiya

A baya dai Iran ta yi shela ranar 19 ga watan Maris cewa ta harbo wani jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35, wani iƙirarin da Washington yi watsi da shi.

Tehran ta kuma yi iƙirari ranar Alhamis cewa ta harbo wani jirgin yaƙin Isra’ila samfurin F-16.

Yankin ya kasance cikin zaman ko ta kwana tun da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da harin sama ranar 28 ga watan Fabrariru, inda suka kashe fiye da mutum 1,340 kawo yanzu, ciki har da jagoran addinin ƙasar Ali Khamenei.

Iran ta rama da hare-haren jirage mara matuƙa da makamai masu linzami kan Isra’ila da Jordan da Iraƙi da ƙasashen Labarawa da ke gaɓar Teku masu kayayyakin sojin Amurka , inda ta haddasa mace-mace da lalata ababen more rayuwa da kuma gigita kasuwannin duniya da harkar sufuri ta sama.