| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Iran 'ba ta ƙarƙare yanke hukunci' kan halartar Kofin Duniya na 2026 a Amurka ba
Rahotanni da ke fitowa daga Iran a ƙarshen watan Afrilu, ta bakin kamfanin dillancin labarai, ISNA mai alaƙa da gwamnatin Iran, suna cewa har yanzu babu tabbaci kan batun.
Iran 'ba ta ƙarƙare yanke hukunci' kan halartar Kofin Duniya na 2026 a Amurka ba
Iran / Anadolu Agency

Har yanzu tana ƙasa tana dabo kan batun halartar Iran gasar Kofin Duniya na FIFA 2026 da zai gudana a Amurka, Canada da Mexico.

Tun bayan fara yaƙin Amurka-Isra'ila kan Iran a ƙarshen Fabrairu, an yi ta samun bayanai masu saɓani daga hukumomin Iran, da tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar, da ma Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA.

Rahotanni da ke fitowa daga Iran a ƙarshen watan Afrilu, ta bakin kamfanin dillancin labarai, ISNA mai alaƙa da gwamnatin Iran, suna cewa har yanzu babu tabbaci kan batun.

An ambato Babban Sakataren Kwamitin Olympics na Iran yana cewa gwamnati ce za ta zartar da hukuncin karshe, yana mai bayyana cewa tawagar kasar na ci gaba da shirye-shiryenta.

Tun da fari, kakakin gwamnatin Iran, Fatemeh Mohajerani ta ce kasar a shirye take don tawagarta ta halarci gasar, kuma an samar da duka shirye-shirye da tsare-tsare kan halartar gasar.

Wani abin lura shi ne, Sakataren Harkokin Waje na Amurka, Marco Rubio ya ce gwamnatin Amurka ba ta dauki wani mataki na hana ‘yanwasan Iran shiga kasar ba, amma ya jaddada cewa wasu jami’ai ‘yan rakiya za su iya fuskantar takunkumin shiga Amurka.

Shugaba Donald Trump  ma ya ce Amurka “ba za ta so ta tsangwami ‘yanwasa ba,” inda ya nuna damuwa kan gamagarin batutuwan tsaro.

Kalamansa sun zo ne bayan rahotannin da ke nuna cewa za a iya maye gurbin Iran a gasar, sai dai daga baya jami’ai sun musanta. Italy ma ta yi watsi da irin wannan tunanin, tana jaddada cewa cancantar zuwa Kofin Duniya dole ya zama bisa hanyar wasa.

Shugaban Hukumar FIFA, Gianni Infantino ya fada ranar 16 ga Afrilu cewa ana sa ran Iran ta halarci gasar, yana tunatar da cewa tawagar ta samu cancatar bugawa kuma ta nuna sha’awar shiga gasar duk da rikicin da ake.

Gasar ta Kofin Duniya FIFA 2026 za ta fara a watan Yuni mai zuwa a Amurka, Canada, da Mexico.