Kungiyar Masana'antar Samar da Lantarki ta Hasken Rana ta Afirka ta ce Afirka ta zama yankin da kasuwar samar da lantarki ta hasken rana ta fi bunƙasa a duniya a shekarar 2025, inda ta yi watsi da koma bayan tattalin arzikin duniya da kuma sake fasalin inda aka fi mayar da hankali kan makamashin da ake sabuntawa.
Rahoton ya nuna cewa ƙarfin shigar lantarki na hasken rana a nahiyar ya faɗaɗa da kashi 17% a 2025, hakan ya ƙru ne ta hanyar shigar da allunan hasken rana daga China.
Ƙarfin samar da lantarki ta hasken rana a duniya ya tashi da kashi 23% a 2025 zuwa 618 GW, wanda ya ragu daga ƙaruwa na 44% a 2024.
"Ci gaban da Afirka ta samu ya samu ne ta hanyar sauye-sauyen manufofi da yanayin tallafi a ƙasashe da dama," in ji John Van Zuylen, Babban Jami'in Zartarwa na Kungiyar Masana'antar Lantarkin Hasken Rana ta Afirka.
Ya ce hakan ne kwanan nan a yayin taron Inter Solar Africa a Nairobi: "Hasken rana ya wuce ƙananan matakai ya zama babban fifiko a fadin nahiyar. Abin da muke gani ba na ɗan lokaci ba ne. Manufofi ne suke daidaita da yanayin kasuwa."
Ƙaruwa a kasuwa a Afirka
A tarihi, Afirka ta Kudu ta mamaye shigar da allunan lantarkin hasken rana a Afirka, ta yadda aka kai wani lokaci da take kan-gaba a amfani da kusan rabin duk allunan lantarkin hasken rana da aka aika zuwa nahiyar.
Amma bayanai na baya bayan nan sun nuna cewa ta yi ƙasa da kashi ɗaya bisa uku yayin da buƙatu ke ƙaruwa a sauran wurare.
A bara, ƙasashe 20 na Afirka sun kafa sabbin tarihi na shekara-shekara na shigar da allunan rana, yayin da ƙasashe 25 suka shigo da jimillar ƙarfin da ya kai akalla megawatt 100.
Nijeriya ta zarce Masar ta zama mai shigar da kayayyakin lantarkin hasken rana ta biyu mafi girma a Afirka yayin da lantarkin hasken rana yake maye gurbin amfani da janareta wanda ya fi laƙume kudi saboda sayen fetur da dizel.
A Aljeriya, shigar da allunan hasken rana ya tashi sama fiye da sau 30 a shekarar-shekara. Shigowar kayayyaki ma sun karu a Zambia da Botswana.
Aƙalla ƙasashe 23 na Afirka, ciki har da Afirka ta Kudu, Tunisiya, Kenya, Chad da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yanzu suna samar da fiye da 5% na wutar lantarki daga hasken rana, in ji rahoton.
Rage farashi
Farashin allunan hasken rana da batira ya sauka sosai, wadanda yawanci daga China ake kawo su, abin da ya ba gidaje da kamfanoni damar dogaro da samun lantarkin hasken rana da batir don samar da wutar lantarki a kowane lokaci, in ji rahoton.
"Wannan ci gaba na ragin farashin baturi na da tasiri sosai ga Afirka, wadda ke da buƙatar gaggawa ta samun wuta mai ɗorewa," in ji Van Zuylen.
Cire tallafin dizel da aka yi a Nijeriya cikin shekaru biyu da suka gabata ma ya taimaka wajen hanzarta karɓar tsarin lantarkin hasken rana, a cewar masana.














