Lauyan tauraron ɗanwasan Paris Saint-Germain ta Faransa, Achraf Hakimi, ya sanar da cewa ofishin mai shigar da ƙara na birnin Nanterre a Faransa ya ba da umarnin yin shari’ar ɗanwasan kan zargin fyaɗe.
Lauyan mai suna Fanny Colin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa za a yi wa Hakimi shari’a ne kan zarge-zargen da wata mata ta masa na cin zarafin jinsi a Fabrairun 2023.
Matar mai shekaru 24, ta yi zargin cewa Hakimi ya mata fyaɗe a gidansa da ke unguwar Boulogne-Billancourt a birnin Paris, ranar 25 ga Fabrairun, 2023, kuma an fara bincike kan lamarin.
Yanzu dai an umarci ɗanwasan mai shekaru 27, wanda ɗan asalin Maroko ne, da ya bayyana a kotun manyan laifuka ta Hauts-de-Seine don fuskantar zargin fyaɗe.
"An ba da umarnin yin shari’a sakamakon zargin da ya dogara kacokan kan kalaman matar da ta ƙi aminta da duka bincike, kuma ta ƙi a yi gwajin likita da na DNA, sannan ta ƙi amincewa a duba wayarta, ta ƙi ba da sunan babban mai shaida," in ji Lauyan.
Martanin Hakimi
Da yake mai da martani kan labarin, Achraf Hakimi ya wallafa a shafinsa na X cewa, "Yau, zargin fyaɗe ya wadatar da fuskantar shari’a duk da cewa na musanta kuma komai ya nuna zargin ƙarya ne. Ina tsanake ina jiran shari’ar da za ta bayyana gaskiya kowa ya gani."
Tun a Satumban bara, rahotannin sun ambato Hakimi yana magana kan batun zarge-zargen a wata hira da gidan talabijin na Canal+ da ke Faransa.
Ya ce, "A wajena, abu ne mai wahala yadda hakan ta faru da ni. Gaskiya ita ce, wannan ne mafi girman ƙalubale da na taɓa fuskanta. Ina jin abin ya kasance kuma yana ci gaba da kasancewa mai wahala gare ni.”
"Lauyana ya gaya min. Mun san wannan zai iya faruwa. Muna cikin tsanaki. Na san abin da ake zargi na. Ƙarya ne. Na san ni wane ne. Na san ban yi komai ba. Kuma ba zan taɓa haka ba."
Achraf Hakimi ya fara ƙwallo ne a Real Madrid kafin ya je Inter Milan, sannan ya zo PSG a 2021 kan dala miliyan $68. Ya ci ƙwallo 66 a wasanni 194 a PSG, inda ya lashe kofin Zakarun Turai.
A matakin ƙasa, Hakimi ya buga wa Maroko sau 93, kuma ya taimaki kasarsa zuwa wasan ƙarshe na kofin Afrika na 2025, wanda Senegal ta doke su.






