Yamal ya sha alwashin cewa za su kafa tarihi a Camp Nou

Lamine Yamal ya yi alƙawarin jan ragamar Barcelona wajen kafa sabon tarihi a filin wasansu na Camp Nou da za su koma buga wasa.

By
A ƙarshen makon nan ne Yamal zai buga wasansa na biyu a filin wasan na Camp Nou

Yayin da Barcelona ke shirye-shiryen komawa filin wasanta na Camp Nou, tauraron ɗanwasan ƙungiyar, Lamine Yamal ya aika saƙo na musamman ga masoyansu.

Yamal ya sha alwashin cewa zai jagoranci Barca wajen kafa tarihin nasarori a filin wasan ƙungiyar da da za a koma buga wasa a ƙarshen mako bayan ya sha kwaskwarima.

An yi wa filin na Camp Nou, gyare-gyaren da suka janyo Barca ta daina buga wasa a filin, kusan kwanaki 900 da rufe shi, duk da ba a kammala gyaran duka ba har yanzu.

Labarin komawar Barca filin wasan mai matuƙar tarihi, yana jan hankalin duniyar ƙwallo, saboda girman filin wajen ɗaukar ‘yan-kallo da kuma damar tara kuɗin tikiti.

Dawowa Camp Nou ya shiga ran Lamine Yamal musamman saboda a yanzu yana hutu, sakamakon barin tawagar ƙasarsa Sifaniya don jinyar cutar matsematsi da yake fama da ita.

Wasan gwaji

Yamal na cike da farin ciki da zumuɗin ranar komawar, inda yake ta wallafa hotunan filin a satin nan, gabanin wasan Barca da Athletic ranar Asabar 22 ga Nuwamba.

Ɗanwasan mai shekara 18 ya buga wasa ɗaya ne tal gabanin rufe filin a watan Agustan 2023, inda a yanzu yake fatan burge ‘yan-kallo a cikinsa.

A saƙon da ya wallafa a Instagram, Yamal ya saka hotonsa yana riƙe da bajon Barcelona kuma ya rubuta cewa, “Camp Nou ne wajen da za a rubuta tarihi.”

Tun bayan Mayun 2023, Barca ta yi ta buga wasa a filin wasanni olympics na Lluis Companys Olympic Stadium a Montjuic. Tun a 2024 aka shirya sake buɗe filin amma bai yiwu ba.

A farkon Nuwamba ne aka yi nasarar gwajin yin wasan atisaye, inda aka bar ‘yan-kallo 23,000 suka shiga. Sai a yanzu ne aka ba su izinin shigar da ‘yan-kallo 45,401.