Shugaban Majalisar Mulkin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya bayyana cewa an cire dakarun Rundunar RSF daga tattaunawar da ta shafi kasa a Sudan, tare da jaddada cewa Rundunar 'Rapid Support Forces' (RSF) ba za ta taka wata rawa a tsarin mulkin kasar bayan kammala yakin ba.
A yayin da yake zantawa da 'yan jarida a wani taron manema labarai a Khartoum ranar Alhamis, Burhan ya ce gwamnati ta kuduri aniyar aiwatar da sakamakon tattaunawar kasa da ke kare muradun al'ummar Sudan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar (SUNA) ya rawaito.
Ya ce wadanda ke halartar tattaunawar na da burin gina ƙasar Sudan ne bisa ginshikin adalci da daidaito, inda ya jaddada cewa tsarin ya takaita ne ga ƙungiyoyin siyasa da na farar hula kawai, kana ba shi da wata alaka da bangaren soji.
Dangane da batun takunkumin hana sayar da makamai da ake sa ran gabatarwa a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kuwa, Burhan ya ce matakin ba zai samu karbuwa ba, kuma ba zai yi wani tasiri ga rundunar sojin Sudan ko matsayinta a fagen daga ba.
Ba a yarda da ƙungiyoyin 'yantawaye ba
Ya kuma bayyana cewa ba za a bai wa duk wata kungiya ‘yantawaye damar samun hanyar amfani da makamai ba, inda ya kara da cewa: "Ba za a ci gaba da samun kungiyoyin 'yantawaye a kasar bayan an kawo ƙarshen yakin ba."
Burhan ya jaddada cewa rundunar RSF ba za ta samu rawar takawa ba a tsarin mulkin Sudan bayan yakin, yana mai nuni da ayyukan take hakkin dan adam da ta'asar da rundunar ta aikata ga al'ummar Sudan.
Ya kuma sake nanata matsayinsa game da Yarjejeniyar Jeddah ta alkawarin kare fararen hular Sudan—wacce Saudiyya da Amurka suka jagoranci cim mawa a shekarar 2023 domin magance rikicin da ke tsakanin rundunar sojin Sudan da RSF—yana mai cewa ita ce ginshiki mai muhimmanci ga duk wata tattaunawa a hukumance kan tsaro ko agaji tsakanin bangarorin biyu.
Burhan ya ce Sudan ta gayyaci jami'an Amurka domin su ziyarci ƙasar su kuma tantance halin da ake ciki a kasa, amma ba ta samu wani martani ba, don haka ya sake sabunta gayyatar.
'Gyara tafarkin juyin juya hali'
A wani bangaren kuma, ya kare matakin da sojoji suka dauka a ranar 25 ga Oktoba, 2021, inda ya ce hakan "ba juyin mulki ba ne" a'a "gyara tafarkin juyin juya hali ne."
Ya zargi gwamnatin farko ta tsohon Firaminista Abdalla Hamdok da gazawa wajen gina kasar, tare da kokarin karfafa jam'iyyun siyasa ta hanyar raunana hukumomin gwamnati.
Burhan ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da ake kara kaimi wajen kokarin kasa-da-kasa na kawo karshen rikicin Sudan.
Inda wata tawaga daga ƙungiyoyin nan biyar na kasa-da-kasa da suka hada da Kungiyar Tarayyar Afirka, da Kungiyar IGAD, da Kungiyar Kasashen Larabawa, da Kungiyar Tarayyar Turai, da kuma Majalisar Dinkin Duniya -- ta kammala ziyarar kwana uku a Khartoum a ranar Alhamis, inda ta tattauna da Burhan da sauran jami'an Sudan kan kokarin kawo karshen yakin da kuma ciyar da tsarin siyasa gaba.
Sudan na fuskantar rikici tsakanin sojoji da rundunar RSF tun watan Afrilun 2023, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyin wasu barin gidajensu.

















