Senegal ta haramta wa jami'an gwamnati tafiye-tafiye marasa muhimmanci zuwa ƙasashen waje
Sakamakon yaƙin Gabas ta Tsakiya wanda ya jawo tashin farashin mai da kayayyaki, gwamnatin Senegal ta dakatar da duk wata tafiya ta ƙasa da ƙasa da ba ta da muhimmanci ga ministoci da manyan jami'ai a ƙasar.
Gwamnatin Senegal ta dakatar da duk wata tafiya ta ƙasa da ƙasa da ba ta da muhimmanci ga ministoci da manyan jami'ai, inda ta yi gargaɗin cewa lokuta "masu matuƙar wuya" na gabatowa.
Yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi kan Iran ya jawo ƙaruwar farashin mai a duniya, inda ya ƙara matsin lamba ga kasafin kuɗin kasashe da dama, kuma yana tilasta wa gwamnatoci ɗaukar matakai don rage illolin.
A yayin jawabi ga matasa a garin bakin teku na Mbour a daren Juma'a, Firaminista na Senegal Ousmane Sonko ya nuna cewa ana sayar da mai kan kusan dala 115 a duk ganga, kusan ninki biyu daga dala 62 da aka yi hasashe a cikin kasafin kuɗin Senegal.
"Babu minista a gwamnatina da zai bar ƙasar sai dai idan akwai muhimmin aiki da ya shafi aikin da muke yi yanzu," in ji shi, inda ya sanar da cewa ya riga ya soke tafiye-tafiyensa da ya shirya zuwa Nijar, Sifaniya da Faransa.
Gwamnatoci a faɗin yankin Yammacin Afirka da ma duniya sun hanzarta mayar da martani ga rikicin ta hanyar ɗaukar matakai kamar ƙara farashin fetur, bayar da tallafi, da kuma bai wa ma'aikata damar yin aiki daga gida.
Sonko ya ambaci irin waɗannan matakan a matsayin hujja ga matakan da gwamnatinsa, mai fama da bashi, ke ɗauka.
Ya ce za a sanar da ƙarin matakai mako mai zuwa, yayin da ake sa ran Ministan Makamashi da Ma'adanai zai yi jawabi ga ƙasa a cikin 'yan kwanaki masu zuwa don fayyace ƙoƙarin rage tasirin wannan tashin farashi.