Sojojin Nijeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar sama ta Operation Hadin Kai sun kai hare-haren sama kan maboyar ’yanta’addan ISWAP da ke yankin dajin Sambisa a Jihar Borno inda aka kashe aƙalla kwamandojin ƙungiyar guda tara.
An gudanar da aikin ne a ranar Asabar, bayan samun bayanan sirri da suka nuna ayyuka da zirga-zirgar wasu da ake zargin ’yanta’adda ne a yankin dajin Sambisa.
Daga cikin waɗanda aka kashe har da Abu Khalid Al Muhajir, wanda aka bayyana a matsayin babban kwamandan ISWAP mai kula da samar da tawagar tsaro ta musamman da ke raka manyan jami’an ƙungiyar ta’addancin yayin zirga-zirgarsu.
Da yake tabbatar da harin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, kakakin rundunar sojin saman Nijeriya, Ehimen Ejodame, ya ce an kuma jikkata wasu ’yanta’addan na ISWAP.

“Bisa bayanan sirrin da aka samu, rundunar sojin saman Nijeriya ta tura wani jirgi mara matuƙi domin gudanar da sa ido, leƙen asiri da bincike a-kai-a-kai. Hakan ya ba rundunar damar gano tare da bibiyar wasu ’yanta’adda yayin da suke tafiya zuwa wata maboya da ake zargin tasu ce.
“Bayan ganowa tare da tabbatar da inda aka nufa, jirgin rundunar sojin saman Nijeriya ya kai hari mai matuƙar inganci kan wurin,” kamar yadda Ejodame ya yi ƙarin bayani.
Jami’in sojan, wanda ke riƙe da muƙamin Air Commodore, ya ƙara da cewa ƙarin bayanan sirri sun nuna cewa wasu daga cikin ’yanta’addan da harin ya rutsa da su na da alaƙa da wasu da ake zargin suna da hannu a kwanton-ɓaunar da aka yi wa sojojin Nijeriya kwanan nan a hanyar Bita–Yamtage, a Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.
Ya ƙara da cewa “binciken da aka gudanar bayan harin ya nuna cewa an samu gagarumar illa a harabar wurin da aka kai wa harin, inda aka kashe wasu ’yanta’adda.
“Ƙarin bayanan sirri da aka samu bayan harin sun tabbatar da cewa an kashe ’yanta’addan ISWAP guda tara, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.”



















