| hausa
AFIRKA
2 minti karatu
An raba fiye da mutum 100,000 da gidajensu a Al Fasher na Sudan daga lokacin da RSF ta ƙwace birnin
Fiye da fararen hula 100,000 ne aka raba da muhallansu a Al Fasher a yammacin Sudan tun lokacin da rundunar RSF ta ƙwace iko da birnin a watan da ya gabata, in ji Hukumar Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya IOM.
An raba fiye da mutum 100,000 da gidajensu a Al Fasher na Sudan daga lokacin da RSF ta ƙwace birnin
Tun ranar 15 ga watan Afrilun shekarar, 2023 ne yaƙi ya ɓarke tsakanin sojin Sudan da rundunar RSF lamarin da aka gza sasantawa. Photo: Reuters
18 Nuwamba 2025

An raba fiye da fararen hula 100,000 da muhallansu a Al Fasher da ke yammacin Sudan tun lokacin rundunar RSF ta karɓe iko da birnin a watan da ya gabata, kamar yadda Hukumar Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM) ta bayyana ranar Litinin.

A wata sanarwar da ta fitar hukumar ta MDD ta ce mutum 100,537 sun tsere daga birnin zuwa wurare 23 a cikin tara daga cikin jihohin Sudan 18.

Hukumar IOM ta ce wakilanta sun ba da rahoton tsananin rashin tsaro a kan hanyoyin da mutanen da aka raba da gidajensu ke bi, lamarin da zai iya hana tafiyar fararen hula.

Daga farkon ranar Litinin dai hukumar MDD mai kula da ‘yan gudun hijira (UNHCR) ta ce ƙarin fararen hula da ke tserewa daga Al Fasher suna isa garin Al-Dabba a arewacin Sudan a ko wace sa’a.

Babban Lauyan gwamnatin Sudan ya ziyarci sansanin mutanr da suka tsere

A wani ɓangare kuma, ofishin mai gabatar da ƙara na gwamnatin Sudan ya karɓo ƙorafi 1,365 daga fararen hula da aka raba da gudajensu a Al Fasher na Arewacin Darfur da kuma jihohin Kordofan game da zaluncin da RSF ta yi musu.

A wata sanarwar da ya fitar, ofishin mai gabatar da ƙarar, ya ce Babban Lauyan Ƙasar Intisar Ahmed Abdel-Aal ya kai ziyara sansaonin ‘yan gudun hijira a Al-Dabba domin nazari kan irin zaluncin da aka yi a Al Fasher da Kordofan.

A watan da ya gabata, RSF ta karɓe iko da Al Fasher, babban birnin Arewacin Darfur, kuma an zarge ta laifin kisan kiyashi. Ƙungiyar tana da iko kan dukkan jihohi biyar na yankin Darfur, daga cikin jihohin Sudan 18, yayin da sojin ƙasar ke riƙe da mafi yawancin sauran jihohi 13, ciki har da Khartoum.

Yankin Darfur dai ya kai kashi ɗaya cikin biyar na ƙasar Sudan, amma yawancin mutanen ƙasar miliyan 50 suna rayuwa ne a wuraren da sojin ƙasar ke iko da su.

Rikicin da ake yi a Sudan tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF, wanda aka fara a watan Afrilun shekarar 2023, ya yi ajalin aƙalla mutum 40,000 tare da raba mutum miliyan 12 da gidajensu, in ji hukumar lafiya ta MDD.

.

 

Rumbun Labarai
Ghana za ta tura injiniyoyin soji don taimakawa wajen sake gina Jamaica bayan afkuwar guguwa
Mutane 70 sun ɓace bayan jirgin ruwa ɗauke da mutum 120 ya kife a DRC
Wata ƙungiya ta zargi kamfanin Nestle da sayar wa Afirka abincin jarirai mai sikari da yawa
Ranar Makewayi ta Duniya: Kundin tsafta na Afirka don inganta lafiya da mutunci
Sabon Alƙalin Alƙalan Ghana Baffoe-Bonnie ya fara aiki
Kafafen watsa labaran Afirka: Abokan kawo ci gaba da ake mantawa da su
Za a ƙara farashin man fetur a Ghana
Ruftawar mahaƙar ma’adanai ta yi ajalin aƙalla mutum 32 a DRC
An samu rahotanni 32 na yi wa 'yan mata fyade bayan RSF ta ƙwace birnin Al Fasher - Likitoci
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na 'yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
DR Congo da M23 sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya 'ta tarihi' a Qatar
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi