An raba fiye da mutum 100,000 da gidajensu a Al Fasher na Sudan daga lokacin da RSF ta ƙwace birnin
Fiye da fararen hula 100,000 ne aka raba da muhallansu a Al Fasher a yammacin Sudan tun lokacin da rundunar RSF ta ƙwace iko da birnin a watan da ya gabata, in ji Hukumar Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya IOM.
An raba fiye da fararen hula 100,000 da muhallansu a Al Fasher da ke yammacin Sudan tun lokacin rundunar RSF ta karɓe iko da birnin a watan da ya gabata, kamar yadda Hukumar Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM) ta bayyana ranar Litinin.
A wata sanarwar da ta fitar hukumar ta MDD ta ce mutum 100,537 sun tsere daga birnin zuwa wurare 23 a cikin tara daga cikin jihohin Sudan 18.
Hukumar IOM ta ce wakilanta sun ba da rahoton tsananin rashin tsaro a kan hanyoyin da mutanen da aka raba da gidajensu ke bi, lamarin da zai iya hana tafiyar fararen hula.
Daga farkon ranar Litinin dai hukumar MDD mai kula da ‘yan gudun hijira (UNHCR) ta ce ƙarin fararen hula da ke tserewa daga Al Fasher suna isa garin Al-Dabba a arewacin Sudan a ko wace sa’a.
Babban Lauyan gwamnatin Sudan ya ziyarci sansanin mutanr da suka tsere
A wani ɓangare kuma, ofishin mai gabatar da ƙara na gwamnatin Sudan ya karɓo ƙorafi 1,365 daga fararen hula da aka raba da gudajensu a Al Fasher na Arewacin Darfur da kuma jihohin Kordofan game da zaluncin da RSF ta yi musu.
A wata sanarwar da ya fitar, ofishin mai gabatar da ƙarar, ya ce Babban Lauyan Ƙasar Intisar Ahmed Abdel-Aal ya kai ziyara sansaonin ‘yan gudun hijira a Al-Dabba domin nazari kan irin zaluncin da aka yi a Al Fasher da Kordofan.
A watan da ya gabata, RSF ta karɓe iko da Al Fasher, babban birnin Arewacin Darfur, kuma an zarge ta laifin kisan kiyashi. Ƙungiyar tana da iko kan dukkan jihohi biyar na yankin Darfur, daga cikin jihohin Sudan 18, yayin da sojin ƙasar ke riƙe da mafi yawancin sauran jihohi 13, ciki har da Khartoum.
Yankin Darfur dai ya kai kashi ɗaya cikin biyar na ƙasar Sudan, amma yawancin mutanen ƙasar miliyan 50 suna rayuwa ne a wuraren da sojin ƙasar ke iko da su.
Rikicin da ake yi a Sudan tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF, wanda aka fara a watan Afrilun shekarar 2023, ya yi ajalin aƙalla mutum 40,000 tare da raba mutum miliyan 12 da gidajensu, in ji hukumar lafiya ta MDD.
.