| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga sun yi garkuwa da ɗalibai 7 daga wata makaranta a Jihar Zamfara ta Nijeriya
Harin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba a yankin Kaura Namoda da ke jihar Zamfara, wadda ta dade tana fama da matsalar tsaro, a cewar kakakin ’yansanda, Yazid Abubakar.
'Yanbindiga sun yi garkuwa da ɗalibai 7 daga wata makaranta a Jihar Zamfara ta Nijeriya
Mutum ɗaya ya tsere a cikin ɗaliban da aka sace / Reuters

Wasu ’yan bindiga sun kai hari wani gidan ɗalibai da ke a wajen makaranta a arewa maso yammacin Nijeriya tare da yin garkuwa da ɗalibai bakwai, kamar yadda ’yansanda suka bayyana.

Harin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba a yankin Kaura Namoda da ke jihar Zamfara, wadda ta dade tana fama da matsalar tsaro, a cewar kakakin ’yansanda, Yazid Abubakar. Daya daga cikin ɗaliban ya tsere kuma yana hannun jami’an tsaro.

Nan take aka tura rundunoni na musamman na ’yansanda tare da sojoji zuwa yankin bayan samun rahoton harin.

Sai dai, kafin jami’an tsaro su isa wurin, ’yanbindigar sun riga sun tsere.

Kakakin ’yansandan ya ce har yanzu ba a san inda aka kai ɗaliban ba, amma ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran shida da aka yi garkuwa da su.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun ƙara kaimi wajen gudanar da ayyukan bincike da ceto domin tabbatar da sakin sauran ɗaliban cikin ƙoshin lafiya tare da kamo waɗanda suka aikata harin.

Jihar Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin yankunan da ƙungiyoyin ’yanbindiga ke yawan aikata satar mutane domin neman kuɗin fansa, yayin da sace ɗalibai ke ƙaruwa a Nijeriya cikin ’yan shekarun nan.

Wata ƙididdiga da kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta tattara ya nuna cewa aƙalla ɗalibai 1,900 aka sace daga makarantu 20 tun bayan sace fiye da ’yan makaranta mata 200 daga Chibok a jihar Borno a shekarar 2014.