Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa a Nijeriya (NAHCON) ta kammala jigilar mahajjatan kasar daga Saudiyya a hukumance bayan gudanar Aikin Hajji na shekarar 2026, wanda ya kawo ƙarshen ɗaya daga manyan ayyukan addinin Islama da ake gudanarwa a duk shekara a ƙasar.
A sanarwa da ta fitar ranar Talata, hukumar ta ce ana sa ran jirgin ƙarshe da ke ɗauke da alhazan Jihar Zamfara ya isa Nijeriya a ranar 23 ga Yuni, wanda da shi za a kammala matakin ƙarshe na dawowar alhazan Nijeriya baki daya daga aikin hajjin bana.
Hukumar NAHCON ta ce nasarar jigilar mahajjatan daga ƙasa mai tsarki zuwa Nijeriya shi ya kawo kammala ayyukan Hajjin 2026.
Ko da yake, hukumar ta bayyana cewa, kawo yanzu mahajjatan Nijeriya 12 suna Saudiyya suna karɓar magani saboda wasu cututtuka daban-daban da suke fama da su.
A cewar hukumar, an tanadi duk wasu shirye-shirye don tabbatar da dawowar su lafiya zuwa gida Nijeriya da zarar an sallame su daga asibiti.
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa nasarar kammala aikin ibadan tare da yabawa da kuma jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima biga goyon bayan da suka bayar.
Ya kuma yaba da kokarin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi, da sauran kamfanonin tafiye-tafiye na alhazai masu lasisi, da abokan hulda na jiragen sama, da kungiyoyin likitoci, da jami'an tsaro, da kungiyoyin manema labarai da kuma mahajjatan Nijeriya saboda gudummawar da suka bayar wajen nasarar wannan aikin.
Kazalika hukumar ta ce an fuskanci wasu kalubale a yayin aikin ibadan amma an koyi muhimman darussa kuma za a yi amfani da su don inganta ayyukan Hajji na gaba.
Haka kuma NAHCON ta soma shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 1448H/2027 a hukumance a matsayin wani bangare na jajircewarta na tsara shirye-shirye da wuri da kuma ci gaba da ingantawa.
Hukumar ta ce an aika da wata takarda mai taken "Soma Shirye-shirye don aikin Hajji na 1448H/2027", ga dukkan shugabanni hukumar a faɗin ƙasar, wanda Sakataren Hukumar, Dr Mustapha Muhammad Ali, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban da Babban Jami'in Gudanarwa na NAHCON.
An umurci hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi, da kwamitoci, da kuma kamfanoni masu gudanar aikin tafiye-tafiye da ke da lasisi, da su fara shirye-shiryen nan take bisa ga ka'idojin da Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta fitar don kakar aikin hajji mai zuwa.
NAHCON ta ce soma shirye-shiryen da wuri zai tabbatar da an samu ingantaccen aikin Hajji a shekarar 2027.















