Harin Isra'ila ya kashe mutum uku a Gaza bayan shafe dare ana ruwan bama-bamai duk da tsagaita wuta

Hukumar Tsaron Al'umma ta Falasɗinu a Gaza ta ce an zaƙulo mutum 3 daga iyalai biyu a cikin ɓaraguzai, sannan an jikkata aƙalla wasu mutane 15 a Khan Younis, a kudancin Gaza.

By
Isra'ila ta kashe Falasdinawa 280 kuma ta raunata 672 tun daga 11 ga Oktoba, a cewar sanarwar ranar Laraba daga Ma'aikatar Lafiya ta Gaza.

Hukumar Kula da Fararen Hula ta Falasɗinu a Gaza ta ce, a safiyar Alhamis an kashe Falasdinawa uku, wasu kuma sun ji rauni a wani harin jiragen sama na Isra'ila da aka kai kan wani gida a kudancin Gaza, abin da ke zama wata sabuwar keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta 10 ga Oktoba.

Hukumar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa tawagarta ta ciro gawawwaki uku da aƙalla mutane 15 da suka ji raunuka daga iyalai biyu bayan harin da aka kai wani gida a Bani Suheila, gabashin Khan Younis a kudancin Gaza.

A ranar Laraba, Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ba da rahoton cewa rundunar sojin Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 25 kuma ta raunata 77 a jerin hare-hare kan wasu yankuna da Isra'ila ta riga ta janye daga cikinsu, abin da hukumomin Falasɗinawa suka ce keta yarjejeniyar tsagaita wuta ce.

Ma'aikatar ba ta fitar da ƙarin bayani kan wuraren da aka kai hari ko ainihin sunayen wadanda abin ya shafa ba.

Keta yarjejeniyar tsagaita wuta

Rundunar soja ta Isra'ila ta ce an kai harin ne a matsayin martani ga harbin bindiga da aka yi wa sojojinsu a Rafah, a kudancin Gaza.

Bayanan da ɓangarorin Falasɗinu da kungiyoyin kare hakkin ɗan adam, da hukumomin gwamnati suka tattara suna nuna cewa Isra'ila ta aikata ɗaruruwan keta yarjejeniyar tsagaita wuta tun bayan da aka fara aiwatar da ita a ranar 10 ga Oktoba.

Tun daga 11 ga Oktoba, Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 280, sannan ta raunata 672, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta fitar a ranar Laraba.

Tun daga farkon yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ta fara a Gaza a watan Oktoba 2023, rundunar sojan Isra'ila ta kashe kusan Falasɗinawa 70,000, mafi yawansu mata da yara, ta raunata sama da 170,000, ta kuma mayar da mafi yawan yankin zuwa ɓaraguzai.