| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Masar ta shigar da ƙorafi gaban FIFA kan alƙalin wasa bayan nasarar Argentina kanta
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Masar ya nemi a binciki gabaɗaya tawagar alƙalai, ciki har da alƙalan bidiyo, saboda kurakuran da suka yi ɓaro-ɓaro.
Masar ta shigar da ƙorafi gaban FIFA kan alƙalin wasa bayan nasarar Argentina kanta
Alkalin wasa Francois Letexier yana nuna wa kocin Masar Hossam Hassan katin rawaya. / REUTERS

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Masar ta sanar ranar Laraba cewa ta nemi a kori tawagar alƙalan da suka jagoranci wasan da Masar ta yi rashin nasara a hannun Argentina da ci 2-3 a wasan zagaye na ‘yan-16 a Gasar Kofin Duniya.

"Hany Aburida, Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Masar, ya shigar da ƙorafi gaban FIFA, yana neman a gudanar da bincike kan alƙali ɗan Faransa, Francois Letexier…, bayan manyan kurakuran alƙalanci da tawagar alƙalai ta aikata da nuna bambanci, wanda ya sa Masar ta yi rashin nasara a wasan, kuma ta fice daga Gasar Kofin Duniya," in ji wata sanarwa daga hukumar.

A daren Talata, Letexes ya soke ƙwallon da Mostafa Ziko ya ci lokacin da suke gaban Argentina da ci 1-0, sakamakon duban da VAR da gano an yi wa Lisandro Martínez ƙeta daga fari.

Minti kaɗan bayan haka, Ziko ya kai Masar gaba da ci 2-0 kuma ta kasance a gaban har zuwa matakin ƙarin lokaci inda aka samu hatsaniya, bayan Cristian Romero da Lionel Messi suka rama ƙwallayen biyu.

Neman yin bincike

Gabanin ƙwallon da ta bai wa Argentina nasarar ta hannun Enzo Fernández, Masar ta yi imanin ya kamata a ce an ba su fanareti saboda jan da Alexis Mac Allister ya yi wa Hamdy Fathy.

"Aburida ya nemi a binciki dukan tawagar alƙalan, ciki har da alƙalan fasahar bidiyo, saboda kura-kurai bayyanannu da kuma ƙin duba wasu daga cikin hotunan da muke ganin suna goyon bayan tawagar ƙwallon ƙafa ta Masar, kuma muna ganin a cikinsu haƙƙin tawagar 'Pharaohs' ne samun halastacciyar ƙwallo da kuma fenareti," in ji sanarwar ta Masar.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ya kuma "nemi a cire alƙalin da dukan tawagar daga Gasar Kofin Duniya, bayan gudanar da bincike kan waɗannan kurakurai da kuma tabbatar da laifin nuna bambanci kan tawagar ƙasar Masar".

Sanarwar ta dace da maganganun mai horar da Masar, Hossam Hassan, da ya yi nan-take bayan wasan.

“An yi mana maguɗi”

Hassan ya shaida wa 'yan jarida cewa, "Ba na son in lulluɓe magana na ce mun yi rashin sa'a. An yi mana maguɗi yau, mun sha rashin adalci".

"Ba mu ga girmamawa ko nuna adalci ba. Babu girmamawa ko nuna adalci."

Hassan ya shaida wa shafin BeIN cewa, "Wataƙila suna son su bar zakarun duniya [na bara, Argentina] a gasar ne. Wataƙila suna son Messi ya ci gaba da kasancewa a gasar."

"A ƙwallon ƙafa, wani lokaci akwai abubuwa daga waje da ke shafar wasan fiye da fannoni ƙwarewa. Zakarun duniya sun samu goyon baya a kowane mataki."