Hare-haren Amurka sun sauka a wuraren da babu 'yan ƙungiyar Daesh a Sokoto, in ji mazauna yankin

Wani ɗan majalisar dokoki ya bayyana ƙauyen Jabo a matsayin wurin da ake da 'zaman lafiya' wanda ba shi da wani tarihi 'na kasancewar 'yan ƙungiyar Daesh, ko Lakurawa, ko ma duk wata ƙungiyar ta'addanci.'

By
Mutane suna duba ginin da ya lalace sakamakon harin Amruka a Offa, Jihar Kwara, ranar 26 ga Disamba, 2025 / Reuters

Mazauna ƙauyen da ke kusa da wurin da Amurka ta kai hari a Jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya sun ce babu wasu mayaƙan ƙungiyar Daesh a yankin, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Mazauna ƙauyen Jabo da ke yankin Tambuwal, sun ce an ji wata babbar ƙarar fashewar bama-bamai tare da turnuƙuwar baƙn hayaƙi da misalin ƙarfe 10 na dare a kusa da ƙauyen nasu, abin da ya sa suka riƙa ficewa daga gidajensu a guje.

“Ba mu iya barci ba a daren da lamarin ya faru. Ba mu taɓa ganin wani abu makamancin wannan ba a rayuwarmu,” a cewar wani mazaunin ƙauyen mai suna Suleiman Kagara, inda ya ƙara da cewa ƙauyensu ba shi da wani tarihi na masu tsattsauran ra’ayi kuma Musulmai da Kiristoci suna zaune cikin lumana a yankin.

“A nan ƙauyen Jabo, muna kallon Kiristoci a matsayin ‘yan’uwanmu. Ba ma rikicin addini, don haka ba mu yi tsammani za a kawo hari ba,” in ji shi.

Bashar Isah Jabo, wani ɗan majalisar dokokin Jihar Sokoto da ke wakiltar Tambuwal, ya bayyana yankin a matsayin “wurin da ake zaman lafiya” wanda ba shi da wani tarihi 'na zaman 'yan ƙungiyar Daesh, ko Lakurawa, ko ma duk wata ƙungiyar ta'addanci.'

Ya ce harin na Amurka ya sauka a wurin da ke da nisan mita kusan 500 daga cibiyar kula da lafiya a matakin farko guda ɗaya tilo da ke ƙauyen, lamarin da ya jefa fargaba a zukatan mazauna ƙauyen ko da yake babu wanda ya jikkata.

Shugaban Amurka Donald Trump ranar Alhamsi ya ce ƙasarsa ta ƙaddamar da gagarumin hari kan 'yan ta'adda na ISIS (Daesh) a Arewa Maso Yammacin Nijeriya, “waɗanda suke kai hari tare da kashe, musamman Kiristoci da ba su ji ba ba su gani ba."

Daga bisani, Rundunar Sojin Amurka da ke Afirka wato AFRICOM ta wallafa wani saƙo a shafin X, tana mai yin ƙarin haske cewa an kai harin ne a "Jihar Sokoto inda aka kashe 'yan ta'addan ISIS da dama".

Kazalika Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta tabbatar da hare-haren da Amurka ta kai a Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar, tana mai cewa da haɗin gwiwar ƙasar aka kai su.