Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 189 tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin 2025 a faɗin duniya saboda karya ka'idojin al'umma da manhajar ta gindaya.
Manhajar Tiktok ta goge bidiyoyi fiye da miliyan 1.5 waɗanda ‘yan Uganda suka wallafa saboda abin da ta kira ‘‘keta dokokin manhajar.’’
A cewar wata jarida a ƙasar da ke yankin gabashin Afirka, an goge bidiyoyin ne daga Tiktok tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin 2025, manhajar ta bayyana cewa suna ɗauke da kalaman kiyayya, da na ƙarya da kuma ba batsa.
Bayan wannan mataki na kwanan nan da aka ɗauka, Uganda ta zama ƙasa ta 29 a cikin jerin ƙasashen duniya da aka fi goge bidiyoyi a TikTok cikin watanni uku.
Bidiyoyi ‘yan Uganda miliyan 1.5 da aka goge ya zarce yawan na ‘yan Kenya 592,000 da aka goge, kasar da ke daya daga cikin ƙasashen duniya da ke amfani da Tiktok a duniya.
Matakin ya shafi dubban mutane
An sauƙe aƙalla bidiyoyi 420,000 na ‘yan Afirka ta Kudu, yayin da aka goge fiye da bidiyoyi 310,000 na ‘yan Nijeriya.
A duniya baki ɗaya, TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 189 saboda karya ka'idojin al'umma na manhajar tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin 2025.
Manhajar TikTok ita ce hanyar sadarwa ta biyu mafi yawan amfani idan aka kwantanta da sauran shafukan sada zumunta a Uganda, baya ga WhatsApp da ake aika saƙonnin cikin sauri.
Hukumar Sadarwa ta Uganda (UCC) ta bayyana cewa ƙasar ta yankin Gabashin Afirka tana da masu amfani da manhajar TikTok mutum miliyan 8.8, wanda ya kai kusan kashi 17% na yawan jama'ar kasar baki daya.
A cewar TikTok, matakin da aka ɗauka na goge bidiyoyin ‘yan TikTok ya shafi waɗanda suka nuna barasa, kwayoyi, da makamai, da kuma yada tsiraici.
A lokuta da dama, bidiyoyin ‘yan Uganda sun sha jan hankali inda aka yi kama mutane a lokuta daban-daban, inda ake zarginsu da amfani da manhajar don cin mutuncin Shugaba Yoweri Museveni da iyalansa.
An yanke wa daya daga cikin wadanda aka zargi, Edward Awebwa, hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari a watan Yulin 2024, yayin da wani, Emmanuel Nabugodi, aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni 32 a watan Nuwamban shekarar saboda amfani da TikTok da yi wajen cin mutuncin iyalan shugaban ƙasar.