Nijeriya da Amurka sun sake jaddada aniyarsu ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa kan harkokin tsaro, yaƙi da ta’addanci, zaman lafiyar yankuna da dangantakar ƙawance bayan wasu manyan tarurruka da aka gudanar a birnin Washington DC.
Mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya jagoranci wata ziyarar aiki ta kwanaki uku zuwa Amurka daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Mayu, inda ya gana da manyan jami’an gwamnatin Amurka ciki har da Mataimakin Shugaban ƙasar J.D. Vance da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio.
Taron ya kuma haɗa da ganawa da Mataimakiyar Sakataren Harkokin Siyasa ta Amurka Allison Hooker da Mataimakin Sakataren Tsaro Daniel Zimmerman, inda suka tattauna kan ƙarfafa haɗin gwiwa wajen yaƙi da ta’addanci, harkokin tsaro, musayar bayanan sirri, ƙarfin tattalin arziki da inganta dimokuraɗiyya.
A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta Nijeriya ta fitar a ranar Asabar, Ribadu ya isar da ƙudirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da ƙarfafa dangantakar ƙawance tsakanin Nijeriya da Amurka.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai wajen magance ta’addanci, tsattsauran ra’ayi, manyan laifukan ƙetare da kuma barazanar hare-haren intanet, musamman a yankin Yammacin Afirka da Sahel.
Bangarorin biyu sun kuma duba ci gaban haɗin gwiwar da ake gudanarwa ƙarƙashin tsarin Nigeria–U.S. Joint Working Group, wanda ke kula da haɗin gwiwar tsaro da tsare-tsare tsakanin ƙasashen biyu.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan inganta musayar bayanan sirri, haɗin gwiwar soja, tsaron iyakoki, tallafin yaƙi da ta’addanci da kuma ƙarfafa hukumomin tsaro na Nijeriya.
Ribadu ya kuma yi wa jami’an Amurka bayani kan sauye-sauyen da gwamnatin Nijeriya ke yi a ɓangaren tsaro, inda ya bayyana tsarin “whole-of-government approach” wanda ya haɗa da matakan soja, hulɗa da al’umma, bunƙasa tattalin arziki, shirye-shiryen kawar da tsattsauran ra’ayi da haɗin gwiwar yankuna domin magance tushen matsalolin tsaro.
Jami’an Amurka sun yaba da rawar da Nijeriya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, tare da bayyana ƙasar a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa ta Amurka a Afirka.
Ƙasashen biyu sun sake tabbatar da aniyarsu ta kare ƙimar dimokuraɗiyya, zaman lafiyar yanki da kuma dorewar zaman lafiya a Yammacin Afirka da yankin Sahel.
Ziyarar ta ƙare da alƙawarin ƙara ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da tabbatar da aiwatar da tsare-tsaren tsaro da ci gaba da aka amince da su tsakanin ƙasashen biyu.









