Kocin Liverpool ya ce burinsu shi ne kammala kakar bana cikin kungiyoyi 4 na saman teburin Firimiya
Kocin Liverpool, Arne Slot ya sallama cewa burin farko na ƙungiyar shi ne kammala kakar bana cikin ƙungiyoyi huɗu na saman teburin Firimiya.
Liverpool ta shiga mawuyacin hali saboda rashin tagomashi a gasar Firimiya ta Ingila, inda a wasanninta tara na ƙarshe ta samu nasara sau biyu kacal.
Wannan ne ya sa kocin Liverpool, Arne Slot ya fara nuna karaya, inda ya ce a halin yanzu burin farko na ƙungiyar shi ne kammala kakar bana ta Firimiya cikin ƙungiyoyi huɗu na saman teburin.
Duk da cewa Liverpool ce ke riƙe da kofin Firimiya na kakar bara, ƙungiyar tana shan wahala a hannun ƙungiyoyin da ke ƙasar teburi.
A halin yanzu, Liverpool tana mataki na tara a yanzu da jimillar maki 22, bayan buga wasanni 14.
Sai dai ko a hakan, maki biyu ne ke tsakaninsu da ƙungiyar da ke mataki na huɗu, wato Chelsea mai maki 24 daga wasanni 14.
Ranar Asabar 6 ga Disamba ne Liverpool za ta kara da Leeds United, kuma gabanin wasan an tambayi Arne Slot game da yanayin da ƙungiyar ke ciki.
Kocin ya ce, "Tabbas burinmu na farko shi ne mu koma cikin ƙungiyoyi huɗu na saman teburi, saboda a fili yake ba ma farin ciki da matsayin da muke a halin yanzu."
Sai a wasa na gabe ne za a ga yadda za ta kaya da Liverpool, musamman ganin ko gwarzon ɗanwasa Mohamed Salah zai buga wasan na ƙarshen makon nan.
Ranar Larabar da ta gabata, Slot bai saka Salah a wasan da suka yi canjaras da ci 1-1 tare da Sunderland ba.