Ministan Kuɗin Benin ya yi nasara da gagarumin rinjaye a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 12 ga watan Afrilu, inda ya samu fiye da kashi 94 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda sakamako na wucin-gadi da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar ranar Litinin ya nuna.
Shugaban hukumar zaɓe, Sacca Lafia, ya bayyana ta gidan talbijin na ƙasar cewa bayan ƙidaya fiye da kashi 90 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, Romuald Wadagni ya samu gagarumin rinjaye.
Lafia ya bayyana cewa Wadagni-Talata ya samu ƙuri’u 4,252,347 yayin da ɗan takarar hamayya Paul Hounkpe ya samu ƙuri’u 269,433, waɗanda daidai suke da kashi 5.95 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.
Hukumar ta ce an haɗa sakamakon ne daga mazaɓu 15,814 daga cikin jumullar mazaɓu 17,463, wanda ya yi daidai da kashi 90.55 cikin 100 na mazaɓun gaba ɗaya.
Lissafin da ba za a iya sauyawa ba
Ta ƙara da cewa “giɓin da ke tsakanin ‘yantakaran ya kai yadda haɗa sauran sakamakon ba zai sauya matsayinsu ba, lamarin da ya sa ba za a iya sauya lissafin sakamakon ba.”
Fitowar masu ƙada ƙuri’u ya tsaya a kan kashi 58.75 cikin , inda masu ƙada ƙuri’u 4,640,354 suka ƙada ƙuri’u daga cikin mutum 7,897,287 da suka yi rajista.
Daga cikin waɗannan , ƙuri’u 4,522,756 ne aka tabbatar cewa suna da inganci, yayin da ƙuri’u 117,598 suka lalace.
Hukumar ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne a faɗin ƙasar da kuma cibiyoyi 14 na ƙada ƙuri’u a ƙetare. Duk da rahotanni na ƙoƙarin katse harkar a wasu wurare a arewacin ƙasar, ta ce dakarun tsaro sun tabbatar da cewa ‘yan ƙasar sun iya zaɓe ba tare da wani tsaiko ba.
Hukumar ta kuma bayyana amfani da wata kafar dijital ta tura saƙonni wadda ta ce ta tabbatar da “iya ganowa ba tare da tsaiko ba da kuma tura bayanai na zaɓe.”
Kotun tsarin mulki
Za a tura sakamako na wucen gadi ga kotun tsarin mulki ba tare da ɓata lokaci ba, wadda ke da iko na ƙarshe wajen tabbatar da sahihaanci da kuma bayyana sakamakon zaɓen.
A ƙarƙashin tsarin zaɓen Benin, hukumar zaɓen ce ke da alhaƙin shiryawa da kuma bayyana sakamakon zaɓe na wucen gadi, yayin da kotun tsarin mulki ne ke da ikon yanke hukunci kan taƙaddama ta zaɓe da kuma tabbatar da sakamakon zaɓe na ƙarshe.
An gudanar da zaɓen ne ranar 12 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar da kuma ƙetare.




















