Manyan ƙere-ƙeren fasaha na Afirka da suka yi tasiri a duniya

Ga kirkire-kirkire da suka samo asali daga Afirka da suka yi shuhura har a wajen nahiyar - una kawo sauyi a fannin fasahar kere-kere, zamantakewar al’umma da raya a'l’adu.

By
M-Pesa ya zama zakaran gwajin dafi wajen nuna yadda za a ba wa marasa galihu damar ta'ammali d akudade da bankuna. / Reuters

Idan mutane suna magana game da kirkire-kirkire a duniya, galibi ana cire Afirka a cikin batun. Amma a tsawon shekaru aru-aru har zuwa zamanin yau, masu tunani da masu ƙirƙira na Afirka sun yi tasiri a duniya a fannoni masu yawa da muhimmanci.

Ga wasu sabbin kirkire-kirkire guda biyar da aka haifa a Afirka waɗanda suka yi ta yawo har zuwa wajen iyakokin nahiyar—waɗanda suka kawo sauyi a fasaha, zamantakewar al'umma, da al'adu.

1. Sarrafa karfe da kira (Kudu da Hamadar Afirka) 

Tun kafin ayyukan sarrafa ƙarfe na Turai ya zama ruwan dare, sassan Afirka sun haɓaka fasahar sarrafa ƙarfe mai inganci bisa kashin kansu.

Aikin ƙarfe a Yammacin Afirka, da kuma a faɗin wasu yankunan kudu da hamadar Sahara, ya bayar da damar samar da ƙarin kayan aiki masu karfi, makamai da kayayyakin more rayuwa—wanda ya haɓaka yawan amfanin gona da ake samarwa, samar da birane, da kuma kafa kasashe.

A zahiri, ƙwarewar sarrafa ƙarfe ta assasa mafi yawan tushen tsarin al'adun Afirka da yawa—kuma a duk fadin duniya an ji tasirin fasahar sarrafa ƙarfe (daga noma zuwa nrka ƙarfe).

2. M-Pesa (Kenya) – Sauyi a fannin aika kudade 

Wataƙila sabuwar fasahar zamani ta Afirka da aka fi sani, M-Pesa (wanda aka ƙaddamar a Kenya a 2007) ta mayar da wayar hannu zuwa cikakken tsarin ta’ammali da kuɗi.

A tsawon lokaci, tsarin ya ba wa masu amfani - har ma waɗanda ba su da asusun banki - damar aika kuɗi, biyan kuɗin wuta ko ruwa, adana kuɗi, da kuma samun basussuka ta hanyar yin amfani da wayoyinsu.

Ga wasu daga cikin tasirinsa:

·        Rungumar ayyukan sarrafa kuɗi a Kenya ya ƙaru daga kusan kashi 26% a tsakanin manya zuwa sama da kashi 80%.

·        An kiyasta cewa M-Pesa ya fitar da kashi 2% na jama’ar na Kenya daga talauci.

·        A shekarar 2023, kashi 59% na ma’aunin GDP na Kenya ya gudana ta hanyar mu'amala da ayyukan M-Pesa.

Tsarin M-Pesa ya zaburar da tsarin kuɗi na wayar hannu da dama a faɗin Afirka da duniya, musamman a wurare masu rauni a fannin tsarin banki da aka saba amfani da shi.

 3. Tulun daukar ruwa na Hippo (Afirka ta Kudu)

Samun tsaftataccen ruwa mai ya kasance ƙalubale a duniya. A shekarar 1991, injiniyoyi biyu na Afirka ta Kudu, Pettie Petzer da Johan Jonker, sun ƙirƙiro ‘Hippo Water Roller’ (wanda aka fi sani da "Aqua Roller")—kwantenar da ke da siffar ganga wadda za a iya tura ta tana gangarawa maimakon ɗaukar ta a ka.

Dalilin da ya sa take da muhimmanci:

·       Yana rage daukar nauyi ga jiki (da hatsarin jin rauni) da ke tattare da ɗebo ruwa sosai.

·       Tsarin yana da sauƙi, mai juriya ne, kuma cikin sauƙi ana iya kai shi zuwa wurare masu nisa ko marasa albarkatu da yawa a duk fadin duniya.

·       An rarraba dubban wannan tulu a tsakanin al'ummomin da ke fama da matsalar ruwa a duk duniya.

Yana zama abinda wani lokaci ake kira "fasahar da ta dace"— mafita da aka tsara don yanayi da ƙuntatawa na al'ummomin gida, amma duk da haka ana iya faɗaɗa amfani da shi a duk duniya.

 4. Lumkani – na’urar gano kamawar gobara a unguwannin talakawa (Afirka ta Kudu)

Na'urorin gano hayaki na yau da kullun galibi suna gaza aiki a cikin gidaje marasa tsari (na unguwannin talakawa) saboda girki da hayaki na yau da kullun na haifar da ƙararrawa ta ƙarya sbaod aba gobra ce ta kama ba, hayakin girki ne kawai. Lumkani, wanda ya samo asali daga Cape Town, ya ƙera na'urar gano karfin zafi wanda cikin sauri ke fahintar zafafar yanayi inda hyaki ba ne, kuma nan da nan sai ya sanar da gidaje makota game da hatsarin yiwuwar samun gobara.

Wasu sakamako da aka samu:

An sanya na'urori sama da 60,000 a Afirka ta Kudu, Kenya, da sauran wurare.

·      An ruwaito cewa ya taimaka wajen iyakance yaɗuwar kashi 94% na gobara a yankunan da aka kai na’urar.

·       An haɗa tsarin tare da ƙananan inshora don taimakawa gidaje masu rauni su murmure bayan tafka asara daga gobara.

Lumkani ya nuna yadda haɗa kayan aiki masu rahusa da ‘yan kuɗaɗen jama’a za su iya magance matsalolin rayuwa da mutuwa a wurare da ke fuskantar ƙalubale.

 5. Lokole – Sadarwa ba da yanar gizo ba don yankuna masu nisa (DR Congo)

A yankunan da ba su da ingantaccen intanet ko wayar hannu, Lokole ya samar da wata hanya mai fasaha: wata cibiyar aika sakon email da sadarwa ba tare da yanar gizo ba da ke ba wa mutane damar ika sakonni a yankunansu cikin sauki,

Mahimmancin tsarin:

•       Yana taimaka wa wajen cike gibin kayan sadarwa na zamani, yana ba da damar sadarwa a yankunan da ba su da isassun ababen more rayuwa.

•       Yana nuna cewa kirkire-kirkiren fasaha a fannin sadarwa ba koyaushe ne yake buƙatar manyan kayan aiki ba - mafita mafi karfi na samuwa ne ta hanyar aiki a yanayin da ake ciki maimakon kalubalantar sa.

•        Lokole (da ayyuka makamantan haka) na nuna makomar samfuran aikin haɗaka mai harshen damo- haɗa hanyoyin sadarwa na gida ba tare da intanet ba tare da samun damar intanet na ɗan lokaci.

Darussa don amfanin gobe

Waɗannan sabbin abubuwa guda biyar da aka kirkira sun daɗe tun daga zamanin baya zuwa zamanin yau, kuma sun shafi kayayyakin more rayuwa na zahiri da fasahar dijital. Amma suna ma’anoni da dama:

•        Halin da aka tsinci kai a ciki abu ne mai ƙarfi - Waɗannan ƙirƙirarrun fasahohin sun samo asali ne saboda ƙuntatawa ta gaske (rashin banki, ƙarancin kayayyakin more rayuwa, hatsarin gobara). Maimakon neman mafita daga waje, masu ƙirƙire-ƙirƙire na Afirka sun mayar da ƙuntatawar zuwa fa'idoji da ke amfanar da jama’a.

•        Sauƙi + rahusa- Da yawa daga cikinsu ba shu shafi fasaha ta birgewa ba, a’a sun zama kaya ne masu saukin sarrafawa, rahusa wajen saya, masu saukin gyara su kuma da za a iya rarraba su a yankuna da dama.

•        Tasirinsa a duniya - Ana kwaikwayon tsarin M-Pesa a duk duniya; sarrafa ƙarfe na ya yi tasiri a tarihin duniya; tulun Hippo da ake gungurawa ya samar da ruwa ga yankuna da yawa.

•        Haɗewar fasahar kere-kere da ta zamantakewa - Lumkani da Lokole sun haɗa fasaha da tsarin zamantakewa.