Iran ta gargaɗi Amurka: 'Za mu ɗauki kowane irin hari a matsayin cikakken yaƙi a kanmu'

Iran ta ce ba za ta bambance tsakanin ƙaramin hari ko babban hari ba inda ta ce idan Amurka ta kai mata hari za ta mayar mata da martani mai ƙarfi.

By
Tehran ta ce ta shirya wa kowane irin yanayi idan Amurka ta kai mata hari / AP

Iran ta ce za ta ɗauki kowane irin hari a matsayin "cikakken yaƙi a kanmu," in ji wani jami'in Iran mai mukami, yayin da kayan aikin soji na Amurka ke shirin isa Gabas ta Tsakiya cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Jami'in, wanda ya yi magana a bisa sharaɗin rashin bayyana suna a ranar Juma'a, ya ce an sanya sojojin Iran a cikin shirin ko-ta-kwana a yayin da ake dakon isowar jirgin ruwan da ke dakon jiragen saman yaƙin Amurka da kuma sauran dakaru.

"Wannan tarin sojin — muna fatan ba da nufin fito-na-fito bane — amma sojojimu sun shirya kan duk wani abu mafi muni," in ji jami'in.

"Shi ya sa komai ke cikin shirin ko-ta-kwana a Iran."

Jami'in ya yi gargaɗin cewa Tehran ba za ta bambance girma ko ƙanƙantar duk wani hari ba.

Ya ce Iran za ta mayar da martani cikin ƙarfi idan aka kai mata hari.

"Kuma za mu mayar da martani a mafi ƙarfi yadda zai yiwu don warware wannan," in ji jami'in.

'Za mu mayar da martani'

Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Alhamis ya bayyana cewa Amurka na da jirgin ruwan dakon jiragen sama da ke hanyar zuwa Iran, amma Trump ɗin ya ce yana fata ba za a yi amfani da jirgin ba.

Jiragen ruwan yaƙin na Amurka ciki har da na dakon jiragen sama na USS Abraham Lincoln, da wasu jiragen saman yaƙi sun fara tafiya a cikin tekun Asia-Pacific a makon da ya gabata.

"Idan Amurkawa suka keta 'yancin Iran da cikakken ikon yankinta, za mu mayar da martani," in ji jami'in. Ya ƙi bayyana takamaiman yadda martanin Iran zai kasance.

"Kasar da ke fuskantar barazanar soja daga Amurka koyaushe ba ta da zaɓi sai ta tabbatar cewa duk abin da take da shi za a iya amfani da shi don mayar da martani, idan zai yiwu, dawo da daidaito kan duk wanda ya yi ƙoƙarin kai hari kan Iran," in ji jami'in.