| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga sun kashe mutum 12, sun yi garkuwa da mata da yara a wani ƙauyen Sokoto a Nijeriya
An ƙona mutum shida ‘yan gida ɗaya ƙurmus a harin, kamar yadda wani mazaunin yankin ga shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters.
'Yanbindiga sun kashe mutum 12, sun yi garkuwa da mata da yara a wani ƙauyen Sokoto a Nijeriya
'Yanbindiga sun kona mutum shida ƙurmus a harin da suka kai wani ƙauye a jihar Sokoton Nijeriya

Wasu da ake zargin ‘yanbindiga ne sun kashe aƙalla mutane 12 tare da sace mata da yara a wani hari da suka kai cikin dare a wani ƙauye da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Nijeriya, a cewar shaidu.

An ƙona mutum shida ‘yan gida ɗaya ƙurmus a harin, kamar yadda wani mazaunin yankin ga shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters.

'Yanbindigar sun shiga ƙauyen Lajinge da misalin karfe 11 na dare a ranar Asabar inda suka buɗe wuta kan mazauna yankin har zuwa karfe 3 na safiyar ranar Lahadi.

Masu AlakaTRT Afrika - Sojojin Nijeriya sun daƙile yunƙurin 'yanta'adda na garkuwa da mutane 31 a Borno

Yankin ya sha fuskantar hare-har daga ƙungiyoyin 'yanbindiga da ke kai hare-hare ƙauyuka, suna sace mazauna yankin don neman kuɗin fansa da kuma sace dabbobi.

"Sun kashe aƙalla mutane 12 tare da jikkata wasu mutum huɗu da kuma sace mata da yara bayan sun yi awon-gaba da dabbobi masu yawa," kamar yadda Auwal Hassan wani mazaunin yankin ya shaida wa Reuters ta wayar tarho.

Tuni dai 'yansanda suka ƙaddamar da bincike kuma nan gaba za a yi ƙarin bayani, a cewar mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Sokoto Ahmed Rufa'i. 

Harin ya zo ne mako guda bayan da 'yanbindiga sun kashe aƙalla manoma 24 a jihar Zamfara mai maƙotaka.