| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar biliyan $700 a ɓangaren haƙar ma'adinai
Ministan Ma’adinan Ƙasa na Nijeriya, Dele Alake, da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, sun sanya hannu kan “tsarin zuba jarin Amurka a albarkatun ma’adinan Nijeriya da darajarsu ta kai dala biliyan 700” a New York.
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar biliyan $700 a ɓangaren haƙar ma'adinai
Nijeriya na da tarin ma’adinin lithium, wanda ke cikin muhimman abubuwan da ake amfani da su wajen kera batir

Nijeriya da Amurka sun ƙulla wata yarjejeniya domin ƙara yawan zuba jarin Amurka a fannin haƙar ma’adinai na Nijeriya, kamar yadda ma’aikatar ma’adinan ƙasar ta bayyana ranar Alhamis.

Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ya rage tallafin ƙasashen waje, inda a maimakon haka ya mayar da hankali kan yarjejeniyoyin zuba jari, musamman a Afirka, inda kamfanonin China ke cikin waɗanda suka fi zuba jari a ƙasashen nahiyar.

Ministan Ma’adinan Ƙasa na Nijeriya, Dele Alake, da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, sun sanya hannu kan “tsarin zuba jarin Amurka a albarkatun ma’adinan Nijeriya da darajarsu ta kai dala biliyan 700” a ranar Laraba a New York, a gefen taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, in ji ma’aikatar.

Masana sun ce ɓangaren haƙar ma’adinai na ƙasashen Afirka da dama har yanzu ya fi karkata ga fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafa su ba, lamarin da ke haifar da ƙalubale ga bunƙasar tattalin arziki.

Sai dai Alake ya ce zuba jarin zai wuce fitar da albarkatun ƙasa kawai, waɗanda darajarsu ba ta kai kayayyakin da aka sarrafa ba.

“Nijeriya ba za ta ci gaba da kasancewa tushen albarkatun ƙasa ba yayin da wasu ke kwashe mafi yawan darajar da ake samu daga cikinsu,” kamar yadda Alake ya bayyana a kafafen sada zumunta.

“Muna son ƙarin sarrafa albarkatun a cikin gida, samar da ayyukan yi masu inganci, ƙarfafa ƙwarewa da kuma samar da ƙarin damarmaki ga ’yan kasuwar Nijeriya.”

Nijeriya na da tarin ma’adinin lithium, wanda ke cikin muhimman abubuwan da ake amfani da su wajen kera batir, kuma yake taka muhimmiyar rawa a sauyin duniya daga amfani da makamashi mai gurɓata muhalli. Hakan ya ƙara jawo hankalin masu zuba jari a fannin haƙar ma’adinai a Nijeriya, ciki har da kamfanonin China.

Washington ta yi ƙoƙarin ƙarfafa hanyoyin samar da muhimman ma’adinai, musamman bayan da China, wadda ke kan gaba wajen samar da su, ta sanya takunkumi kan fitar da wasu daga cikin ma’adinan da ba kasafai ake samu ba a bara.

Nijeriya na kuma da ma’adinan zinariya, tin, duwatsu masu daraja, ƙarfe da phosphate.

Ma’aikatar ta ce a cikin wata sanarwa: “Ana sa ran yarjejeniyar za ta yi amfani da alaƙar gwamnatocin Najeriya da Amurka a matsayin ginshiƙin samar da yarjejeniyoyin kasuwanci tsakanin kamfanoni.”

Dangantakar Washington da Abuja ta kasance cikin rashin daidaito, inda Trump a bara ya bayyana yawan tashe-tashen hankula da ake samu a arewacin Nijeriya mai rinjayen Musulmi a matsayin “kisan kare-dangi” da ake yi wa Kiristoci.

Gwamnatin Nijeriya da wasu manazarta masu zaman kansu sun yi watsi da waɗannan zarge-zarge, lamarin da ya haifar da takaddamar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Sai dai daga baya hakan ya haifar da ƙarin haɗin gwiwar soji da kuma tura sojojin Amurka zuwa Nijeriya.