Ƙasashen Afirka sun yunƙura don kare jama'arsu da ke Gabas ta Tsakiya

Ƙasashen Afirka da dama sun nuna damuwa tare da fara ɗaukar matakai daban-daban domin ganin sun kare jama'arsu daga rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.

By
Dubban fasinjoji sun makale a filayen jiragen sama yayin da rikici ke ƙara ta'azzara a yankin. / AP

Gwamnatocin wasu ƙasashen Afirka sun ɗauki matakai cikin gaggawa don kare 'yan ƙasarsu yayin da tashin hankali tsakanin Iran, Isra'ila da Amurka ke ƙara tsananta zuwa abin da masana ke kira mafi mummunan rikicin yankin a cikin shekaru.

Rikicin, wanda harin haɗin gwiwar da Isra’ila da Amurka suka kai a kan Iran wanda ya kai ga kashe Jagoran Addini a Iran Ali Khamenei, inda Iran ɗin ta biyo baya da harin ramuwar gayya daga Iran, ya janyo mummunan cikas a zirga-zirgar jiragen sama ta duniya, har aka rufe manyan filayen jirgin sama na ƙasa da ƙasa.

Afirka ta Kudu na rokon 'yan kasa su yi rijista

A Afirka ta Kudu, gwamnati ta bukaci duk 'yan ƙasar da yanzu suke Gabas ta Tsakiya da su gaggauta tuntuɓar ofishin jakadancin Afirka ta Kudu a kasashen da suke domin a san inda suke.

Ma'aikatar Hulda da Kasashen Waje da Hadin Kai (DIRCO) ta yi gargaɗin cewa rufe sararin samaniya ya bar wasu 'yan kasar a makale kuma tana sane da cewa taimakon ofishin jakadanci ba zai kasance yadda ake so ba a irin wannan lokaci na gaggawa.

Mai magana da yawun DIRCO, Clayson Monyela, ya ce hukumomi suna ci gaba tuntuɓa da 'yan Afirka ta Kudu ta amfani da dandalin sadarwa daban-daban.

"Tsarinmu yana aiki. Kowane ofishin jakadanci yana da tsarin kwashe ‘yan ƙasarsa. Ana duba hanyoyi da zaɓi daban-daban.

“Muna shawartar waɗanda suke da rajista da mu su fice," in ji shi a X, yana karawa da cewa waɗanda suka yi rijista da ofishin jakadanci an riga an tuntube su—kafin harin na baya-bayan nan.

Uganda na shawartar 'yan kasa su bar Iran

Uganda ta ƙara gaba inda ta roƙi 'yan kasar da suke Iran da su ɗauki matakan gaggawa na tsaro kuma su bar ƙasar idan zai yiwu. Kampala ta kuma tabbatar da janye ma'aikatan ofishin jakadancinta waɗanda ayyukansu ba muhimmai ba.

A wata sanarwar tsaro, Ma'aikatar Harkokin Waje ta Uganda ta ce tana bibiyar al'amura "da matukar damuwa" kuma ta buƙaci dukkan ɓangarori su nuna natsuwa da fifita tattaunawa.

Ghana ta dakatar da zirga-zirga maras muhimmanci

Gwamnatin Ghana ta dakatar da duk wata zirga-zirgar da ba ta muhimmanci zuwa Gabas ta Tsakiya, inda ta bayyana cewa akwai yiwuwar ƙarin tashin hankali da hadarin zirga-zirgar jiragen sama da na teku sun karu.

Accra ta nuna damuwa cewa rufe sararin samaniya kwatsam na iya barin matafiya a makale a yankunan da ake fafata yaƙin.

An roki 'yan Ghana da suke yankin—musamman a ƙasashen Gulf, Isra'ila da Lebanon—da su guji wuraren soja da taron jama'a masu yawa, kuma su yi rajista da ofishin jakadanci ko ƙaramin ofishin jakadanci mafi kusa.

An saka ofisoshin diflomasiyya cikin halin ko-ta-kwana yayin da hukumomi ke sabunta bayanan su don sauƙaka yiwuwar kwashe jama'a.

Shawarar ta zo ne yayin damuwar da ake da ita game da yiwuwar toshe Mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanya ga jigilar mai ta duniya, wanda hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin Afirka da ke dogaro da daidaitar farashin makamashi da hanyoyin kasuwanci.

Kenya ta yi kira da a yi taka-tsantsan

Kenya ma ta fitar da gargadi na tafiye-tafiye da tsaro bayan rahotannin harbe-harbe a Iran da martani na ramuwar gayya.

Ma'aikatar Harkokin Waje da Al'ummar 'Yan Diaspora ta bukaci 'yan Kenya dake Iran, Isra'ila, Qatar, UAE, Bahrain, Kuwait, Saudi Arabia, Jordan da Iraq da su yi matukar taka tsantsan, su guji zirga-zirgar da ba ta da muhimmanci—musamman a kusa da sansanonin soja—kuma su rika sa ido sosai kan sanarwar hukuma daga kasashen da suke.

Sakataren Harkokin Wajen Kenya Musalia Mudavadi ya ce Nairobi na ci gaba da tuntuɓar ofisoshin jakadancinta a yankin kuma zai rinƙa bayar da bayanai dangane da abubuwan da ke faruwa. An bukaci 'yan Kenya da ba su yi rajista ba su je ofishin jakadanci mafi kusa su yi.

Tarayyar Afirka ta yi gargaɗi

A matakin nahiyar, Tarayyar Afirka ta yi kira ga tsagaita wuta saboda tsoron cewa dogon rikici zai iya haifar da mummunan sakamako ga Afirka.

Shugaban Kwamitin AU, Mahamoud Ali Youssouf, ya yi kira da "tsahirtawa, gaggawar rage tashin hankali da ci gaba da tattaunawa," yana gargaɗin cewa ƙara tashin hankali zai iya ƙara taɓarɓarewar zaman lafiya a duniya.

Ya yi gargaɗin cewa sakamakon rikicin na iya tarwatsa kasuwannin makamashi, kawo matsalar samar da abinci da rage ƙarfin jurewar tattalin arziki—musamman a Afirka, inda kasashe da dama ke fama da rikice-rikice da matsin tattalin arziki.